NARTO suna ƙoƙarin wajen wayar da kan direbobi – Muhammad Inuwa

Daga MUHAMMADU MUJITTABA a Kano

Alhaji Muhammad Inuwa Sakataren Ƙungiyar Masu Motocin Sufuri na Ƙasa, rashen Jihar Kano ya bayyana cewa, ƙungiyar su ta NARTO na taka muhimmiyar rawa wajen ganin ma’aikatan su sun bi duk kanin ƙa’idojin tuqi da kuma kula da lafiyar ababan hawan su a koda yaushe domin ganin an rage munanan haɗurran da akan samu akan hanyoyinmu na Nijiriya musamman a watanni huɗu ƙarshen kowacce Shekara.

Kamar dai yadda sakataren ƙungiyar NARTO na Kano ya bayyana a lokacin taron wata ƙungiya mai suna MAMA da ta shirya don wayar da kan masu tuƙa ababan hawa da gayyato hukumomi da aungiyoyi masu ruwa da tsaki akan fannin tuqi a Nijiriya.

Haka kuma sakataren NARTO na Kano Muhammad Inuwa ya ƙara da cewa, suna ziyartar tashoshi da kasuwanni domin yin gangami na tara masu tuƙa ababan hawa su tunatar da su, muhimmancin bin ƙa’idar tuƙi da kuma illar ganganci da rashin nutsuwa ko shaye-shaye ga masu tuƙa ababan hawa akoyaushe, inda ya yabawa hukumomi masu ruwa da tsaki wajen tabbatar da an bi dokokin tuƙi.

A ƙarshe, jami’an hukumomin kula da bin ƙa’idar tuƙi da suka hallarci taron irinsu K Abubakar Ibrahim Imam daga MTD Kano, sai Isah Musa da Sauran su ne su ka yi dogon bayani wajen yadda za a kare afkuwar haɗurran ganganci a Nijiriya.