Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Masu buƙata ta musamman a jihar katsina sun koka akan rashin wakilcinsu a majalisar zartaswa na gwamnatin Gwamna Dikko Umar Raɗɗa.
Hakan na faruwa ne duk da cewa an aiwatar da doka da ta bada kulawa na musamman a Nijeriya a lokacin gwamnatin Muhammadu Buhari da ta wuce.
Shugaban ƙungiyar masu buƙata na musamman reshen jihar, Nasiru Dauda ‘Yansiliyau ya faɗa wa manema labarai haka da yake magana akan ranar masa buƙata ta duniya.
“Kasancewar su masu buƙata ta musamman a madafun iko shine zai ƙara kwantar masu da hankali da kuma rage tsangwama daga al’umma,” ya ce.
Malam Nasiru Dauda ya bayyana harkar ilimi, kiwon lafiya tsangwama a matsayin wasu daga matsalolin da suke fuskanta.
Sai dai kuma shugaban ya yaba wa Gwamna Dikko Raɗɗa da sanya mambobinsu cikin malaman S POWER da gwamnati ta ɗauka aiki.
Sai ya yi kira ga gwamnatin jiha da ta duba yiwuwar bayar da alawus-alawus ga masu riƙe da sarautun gargajiya masu buƙata ta musamman tare da samar masu da kayayyakin koyon sana’o’i domin dogaro da kai.
Ya kuma roƙi gwamnan da ya naɗa mataimaki na musamman akan masu buƙata ta musamman domin sauƙaƙa masu matsalolinsu su kuma san ana yi da su.
