Raɗɗa ya jagoranci jami’an tsaro wajen shiga daji don farautar ‘yan bindiga a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamna Dikko Umar Raɗɗa na jihar Katsina tare da ayarin jami’an tsaro sun shiga dajin Zakka domin farautar ‘yan bindiga.

An dai yi arangama da ‘yan bindigan da jami’an tsaron inda jami’an tsaron suka samu nasarar kuɓutar da wani mutum ɗan shekara talatin da uku.

Gwamnan ya je karamar hukumar Safana a bisa gayyatar mataimakin kakakin majalisar dokoki na jihar don ƙardamar da bada tallafin kayan abinci da mataimakin kakakin majalisar ya samar.

Ana cikin bikin bada tallafin ne sai gwamnan ya samu labari shigowar ‘yan bindigan garin Zakka inda nan take ya bi ayarin jami’an tsaron inda suka samu nasarar fattakan ‘yan bindigan.

Sai dai bayan an yi batakashi jami’an tsaron sun samu sun fatattaki ‘yan bindigan.

Gwamna Raɗɗa nan take ya bada umurni akai shi wanda ‘yan bindigan da suka harba a kafa zuwa asibitocin samun kulawa na gaggawa.

Al’ummar garin Zakka sun nuna jin daɗinsu da ganin gwamnan da kansa ne tare da jami’an tsaron suka kawo masu ɗauki na fatattakarsu ‘yan bindigar.

Gwamnan dai a lokacin da yake yaƙin neman zave ya sha alwashin cewa idan yanci zaɓe shi da kansa zai jagoranci ayarin jami’an tsaro shiga daji wajen fatattakar ‘yan bindigar.

By Editor