Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Al’ummar ƙauyen Tudun Biri da ke Jihar Kaduna sun yi tutsu bisa ƙarar da aka shigar da sunansu a Babbar Kotun Tarayya Kaduna ta neman Gwamnatin Tarayya ta biya su diyyar Naira biliyan 33 kan kuskuren harin boma-bomai da aka kai, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da 100 tare da jikkata wasu da dama.
Dagacin ƙauyen Tudun Biri, Malam Balarabe Garba, ne ya bayyana haka a lokacin da ya kai ziyarar godiya ga Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, inda ya ce, sun samu labarin cewa, wasu sun garzaya kotu a madadinsu.
Ya ce, “wani wanda ya yi iƙirarin cewa shi ɗan kauyen ne mai suna Ɗalhatu Salihu a madadin mutanen Tudun Biri, ya shigar da ƙara ta hannun lauya mai suna Mukhtar Usman a babbar Kotun Tarayya da ke Kaduna, inda ya buƙaci a biya su diyya.
“Ba mu cikin wannan, ba mu goyi bayan hakan ba kuma ba mu tura kowa zuwa kotu ba.
“Mu mutane ne masu zaman lafiya kuma ba ma goyon bayan kai gwamnati kotu. Mun ji daɗin yadda Gwamnatin Jihar Kaduna da ta tarayya suka ɗauki mataki bayan tashin bom ɗin.
“Gwamnatin Tarayya da Gwamnatin Jihar Kaduna sun ɗauki matakai da dama kuma sun yi alƙawurra, waɗanda ba mu san irin godiyar da za mu yi musu ba, saboda goyon bayan da suka bayar.”
Malam Garba ya ce, al’umma da mutanen da tashin bom ya shafa kai tsaye sun bayyana cewa ba su da masaniya kuma ba su umurci kowa ya shigar da ƙara a madadinsu ba.
“Duk da haka, sun roƙi cewa baya ga alƙawura daban-daban, suna da waɗanda suka kammala karatunsu ba su da aikin yi, waɗanda ya kamata a taimaka musu da ayyukan yi,” inji basaraken ƙauyen.
Shi ma da yake nasa jawabin, jagoran mabiya addinin Kirista a Tudun Biri, Rabaran Musa Sa’idu, ya yaba wa gwamnatin Jihar Kaduna da Gwamnatin Tarayya bisa matakan da suka ɗauka na tallafa wa al’ummar yankin kan haxarin.
Ya ce, “muna da haɗin kai kuma muna yin abubuwa tare. Babu yadda za mu goyi bayan kowa ya ɗauki mataki kan gwamnatin da ta kawo mana agaji.
“Gwamnati na yin duk mai yiwuwa, don tabbatar da jin daɗin al’umma. A madadin Kiristocin da ke Tudun Biri, ba mu umarci kowa ya kai gwamnati kotu ba.”
A nasa ɓangaren, babban limamin Tudun Biri, Malam Hashim Ja’afaru, ya ce, sun ji daɗin abin da gwamnati ke yi game da lamarin, kuma za su mara wa gwamnati baya don cika alƙawuran da ta ɗauka.
Ya ce, “Mu ‘yan uwan mutanen da lamarin bam ya shafa, mun zo nan ne domin ganawa da gwamnan jihar Kaduna domin mu nuna jin daɗinmu ga gwamnatin jihar kan goyon bayan da ta ba mu.
“Ba mu umurci kowa ya kai gwamnati kotu ba, duk wanda ya yi hakan ba daga garemu ba ne, ba mu san shi ba, kuma yana yin hakan ne ba tare da izininmu ba. Muna kira ga gwamnatin jihar da ta nemo shi kuma a bar doka ta ɗauki matakin.”
Da yake mayar da martani, Sani ya ce ɓangarori da dama sun yi ƙoƙarin ganin bam ɗin ya zama wani abu addinanci ko kuma a siyasantar da lamarin, ya ƙara da cewa, “amma kasancewar ɗaya daga cikin al’ummomin da ke da haɗin kai a jihar Kaduna, al’ummar da suka jajirce sun bijirewa duk wani abin da ya faru.
“Tazarar da ke tsakanin Cocin su da Masallaci bai wuce mita 100 ba. Tunanin duk wanda ya je kotu a madadin iyalan waɗanda aka kashe ba gaskiya ba ne. Al’ummar sun buƙaci mu binciki lamarin kuma duk wanda aka samu da hannu zai fuskanci shari’a.”
Sani ya ba su tabbacin cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da ba su goyon baya, inda ya ce, “za a kafa wani kwamiti da zai yanke shawarar yadda za a raba kuɗaɗen da aka ba su na ‘yan Nijeriya masu kishi.
“Muna so ku kawo mutum biyar daga cikin al’ummarku a matsayin mambobin wannan kwamiti.
“Taimakon zai tafi kai tsaye ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu da kuma waɗanda ke asibiti.”
Sani ya kuma yaba wa iyalan waɗanda abin ya shafa bisa jajircewar da suka nuna na bijire wa ƙoƙarin da wasu ’yan kasuwar addini ke yi masu son yin amfani da wannan abin takaici wajen haddasa rashin jituwa a tsakanin al’umma.
