Biyan diyyar rusau: Gwamnatin Kano ta miƙa wuya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Jihar Kano a ƙarƙashin jagorancin Abba Kabir Yusuf ta miƙa wuya, inda amince za ta biya diyyar Naira Biliyan Uku ga ƙungiyar masu shagunan masallacin idi da ke birnin Kano, saboda rusa musu kadarorin da aka yi musu ba bisa ƙa’ida ba.

An cimma yarjejeniyar ne ta wata takardar neman sasanci a ranar 12 ga Disamba tare da gabatar da ƙara a ranar 13 ga Disamba ta hannun lauyoyi a gaban Mai Shari’a Inyang Ekwo na Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja
Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya ya bayyana hakan ne biyo bayan rushe shagunan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi.

Masu shagunan sun kai ƙarar gwamnatin jihar da hukumar tsare-tsare ta Jihar Kano (KNUPDA); babban lauyan gwamnati, Rundunar ’Yan Sanda; Mataimakin Sufeto Janar Na ‘Yan Sanda Shiyya Ta 1 Da Ke Kano; Kwamishinan ’Yan Sanda, Kano; Kwamandan Hukumar Tsaro Ta Farar Hula (NSCDC) ƙara.

Mai Shari’a Samuel Amobeda, a ranar 29 ga Satumba a wani hukunci da ya yanke, ya umarci gwamnatin jihar ta biya ‘yan kasuwar Naira Biliyan 30 a matsayin diyyar Naira Biliyan 250 da ‘yan kasuwar ke nema, kan rushe musu kadarorin da aka yi.

Amma sakamakon ƙin bin umarnin kotun Kano da gwamnatin jihar ta yi, ‘yan kasuwar sun shigar da ƙarar a gaban Mai Shari’a Ekwo, inda suka nemi a tilasta wa gwamnatin biyan su.
Hakan ne ya sa kotu ta bayar da umarnin rufe asusun ajiyar bankin gwamnatin jihar kan ƙin bin umarninta.

Sai dai kuma da aka ci gaba da sauraren ƙarar a ranar Alhamis, lauyan masu ƙara, Dokta N. A. Ayagi, ya shaida wa kotun cewa ɓangarorin biyu sun cimma matsayar biyan kuɗin.

Daga nan sai Ayagi ya buƙaci kotun da ta amince da shirin sansancin cikin masalaha.

Har ila yau, kasancewar lauyan waɗanda ake kara, Affis Matanmi, bai yi jayayya kan hakan ba kuma bai ƙalubalaci batun ba, don haka Alƙali Ekwo ya yanke hukuncin kamar yadda ɓangarorin biyu suka aminta.

By Editor