Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce za ta gurfanar da wata mata da ake zargi da laifin cin zarafin ɗiyar kishiyarta mai shekaru 12 a garin Tsafe da ke yankin ƙaramar hukumar Tsafe a jihar.
Kwamishinar mata, yara da cigaban al’umma ta jihar ta Zamfara, Dr Nafisa Muhammad, ta bayyana hakan a lokacin da ta ziyarci wanda abin ya shafa.
Kwamishinar ta ce, “mun samu rahoton cewa wata Aisha Mustapha da ke garin Tsafe ta yi wa ɗiyar kishiyarta ‘yar shekara 12 illa ta hanyar narka leda a jikinta tare da tilasta mata shan fitsari.”
Nafisa ta sha alwashin cewa gwamnatin jihar Zamfara ba za ta amince da irin wannan cin zarafi ba, tana mai jaddada cewa za a gurfanar da matar da ake zargi a gaban kotun da ta dace.
Mahaifiyar yarinyar, Malama Maryam Muhammad, ta roƙi gwamnatin jihar da ƙungiyoyi masu zaman kansu da ke aiki a jihar da su binciki duk ta’asar da ake zargin wadda ake zargin ta aikata.
Ta bayyana godiyarta ga kwamishiniyar da jami’an ƙungiyoyi masu zaman kansu kan yadda suka nuna damuwarsu da goyon bayan da suka bayar game da halin da ‘yar tata ta shiga.
