Kasafin kuɗin Ma’aikatar Tsaro na 2024 ya yi kaɗan – Badaru

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Ministan Harkokin Tsaro, Abubakar Badaru, ya roƙi Majalisar Tarayya su ƙara wa ma’aikatarsa kason kuɗaɗe cikin kasafin 2024.

Ministan ya yi wannan roƙo ne a ranar Laraba, lokacin da ya bayyana a gaban Kwamitin Majalisar Dattawa da na Tarayya, a wani zaman tare da suka yi, a Majalisar Ƙasa, a Abuja.

Badaru da bayar da dalilan da suka haɗa da tashin tsadar gudanar da ayyukan sojoji, ƙarin farashin dizal da fetur da sauran dalilai.

Cikin kasafin 2024 dai an ware wa Ma’aikatar Tsaro Naira bilyan 78.5 domin biyan albashin sojoji da kuma gudanar da ɗawainiyar ofis.

Sai dai kuma Ministan ya ce kuɗaɗen sun yi kaɗan a wurin yaqi da matsalolin tsaro da ke addabar faɗin ƙasar nan.

Ya ce matsalar tsadar rayuwa da ake fama da ita ce ta ƙara sa farashin komai ya yi tsada a halin yanzu.

Shugaban Kwamiti na Ɓangaren Majalisar Dattawa, Ahmad Lawal ya nemi jin dalilin da ya sa har yanzu ba a fara shirin tsaron makarantu da Sojojin Nijeriya za su yi, duk kuwa da irin matsalar da tsaron da ke ƙara buwayar Nijeriya.

Sai dai kuma har kwamitin ya tashi, Minista Badaru bai bayar da amsa ba.

By Editor