Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Gwamnatin Nijeriya ta bayar da tabbacin daukar mataki kan likitoci da sauran mutanen da ke da hannu a harkar safarar koda.
Jami’ar yada labarai ta ma’aikatar lafiya ta kasar, Ms Patricia Deworitshe ce ta bayar da tabbacin cikin wata sanarwa da aka fitar ranar Laraba a Abuja, babban birnin Nijeriya.
A cewar jami’ar, gwamnati ta sanar da kudirinta na ladabtar da duk wanda aka kama da hannu a safarar koda bayan rahoton da jaridar Daily Trust ta wallafa kan yadda ake yin harkar a boye.
Ta ce “ma’aikatar ta yi tir da irin wannan mummunar dabi’a ta safarar koda kamar yadda rahoton na Daily Trust ya bayyana.
Ma’aikatar lafiyar ta kuma tunatar da mutane game da sashe na 51 zuwa 56 na dokar lafiya ta kasa da ya haramta safarar qodar.
“Mutanen da suka ki bin dokar sun aikata laifi kuma za su iya fuskantar biyan tarar naira miliyan daya ko zama gidan yari ko ma duka biyun.
Ms Patricia Deworitshe ta ce hukumar kula da aikin likitoci ta Nijeriya tana duba zarge-zargen da aka yi kan likitoci da suke wannan ta’adar.
Deworitshe ta kara da cewa kamata ya yi bayar da gudummawar koda ya zama bisa masaniyar wanda zai ba da kodar tasa, kuma bisa shawarar likita.
