Gobe Tinubu zai yi wa ‘yan ƙasa jawabin sabuwar shekara

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Gobe Litinin, 1 ga Janairu, ake sa ran Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu zai yi wa ‘yan kasa jabi albarkacin shiga sabuwar shekarar 2024.

Kakakin Shugaba Kasa, Ajuri Ngelale, ya bayyana a sanarwar da ya fitar yau Lahadi cewa, da karfe 7:00 na safe ne ake sa ran Shugaban ya gabatar da jawabin nasa.

“Don haka ake kira ga tashoshin talabijin da na rediyo da sauran kafafen yada labarai da su jona da tashoshin talabijin da rediyo na gwamnati don yada jawabin,” in ji shi.

Wannan shi ne karon farko da Tinubun zai yi wa ‘yan kasa jawabin shiga sabuwar shekara tun bayan da ya kama mulki a watan Mayun 2023.

By Editor