Neman aure: Kowacce ƙwarya da abokiyar burminta (2)

Spread the love

Tare da AMINA YUSUF ALI

Barkanmu da sake haduwa a wani makon a shafinku na zamantakewa a jaridarku mai farin jini Blueprint Manhaja.

A wannan mako za mu cigaba da tattaunawa a maudu’in da muka fara a makon da ya gabata. Wato yadda ake yawaitar samun  samari da ‘yammata/zarawa marasa aure a garin nan. Bayan kuma ba wani abu suka rasa da za a ce ana son su ba ko a aure su.

A makon da ya gabata mun fara tattaunawa a kan wannan lamari har muka fara kawo muku wasu daga cikin dalilan da suke jawo haka, yanzu kuma za mu cigaba daga inda muka tsaya a wancan makon. A sha karatu lafiya.

Dalili na gaba shi ne, fasalin mace ko namijin da ake so: kamar yadda Bahaushe yake cewa, wai shan koko daukar rai, ra’ayin mutum yana tasiri matuqa wajen zadar abokin rayuwar aure. Kowanne dan’adam, walau mace ko namiji yana da ra’ayinsa game da wanda ko wacce zai aura.

Sai kalilan wadanda suke duba halayyar wanda za su aura. Su  ajiye ra’ayin nasu a gefe. wasu matan sun fi son kyakkyawan namiji ko su ce dogo, wasu su ce sun fi son mai saje, wasu kuma su ce  fari ko baki da sauransu. Hakan su ma mazan sukan ce sun fi son fara, ko baka, ko mai tsawo, ko gajera, ko siririya, ko mai kiba, da sauransu.

Amma inda matar ke ka da mijin shi ne, ita wacce kake son kai ka yi mata? Ko ke wanda kike ra’ayin ina za ki samo shi? Shi ya sa sai a yi ta lalube wani a dace a kusa, wani a samu jinkiri sannan a dace, wani ma kuma sai dai a hakura da abinda ya samu.

Sanayya tana kawo raini: Wasu kuma suna kin auren na kusa da su kamar a dangi ko makwabta ko abokan aiki saboda gudun kada a raina su. Wato suna ganin wanda ya san asalinka har ma ya san wasu abubuwa masu kyau da marasa kyau da suka faru da rayuwarka ko zuriyyarku to zai iya goranta maka ko miki nan gaba a rayuwa.

Ko kuma kai din ko ke din kun tava aikata wani abu na Allah wadai a rayuwarka/ki wanda makusantanku suke tsoron hada nasaba da ku. Duk da dai kamata ya yi a dinga uzuri ga wanda ya tuba da aikata wani laifi.

Rashin sana’a ga maza: Su kuma maza wani lokacin ga ‘yammatan sun samu a hannu. Amma rashin sana’ar da za su hada kayan auren sun zama cikas a wajensu. Ko da ya fara neman yarinya idan aka nemi ya fito ya ki, za a dauke shi mayaudari kuma a dakatar da shi.

Idan kuma aka samu wanda yake da sana’a ya fito yana sonta, sai ka ga an ajiye shi gefe an ba da yarinyar ga wanda yake da sana’a. A nemi sana’a maza!

Cimma buri: Wasu mazan ko matan suna son su yi auren amma akwai wasu burika da suke son cimmawa kafin au yi aure. Akwai darussa da yawa a makaranta wadanda ba a hada su da aure. Irin wannn yana sa a yi ta ganin mace kamar tana korar samari. Amma ni a ra’ayina aure ba ya hana ilimi. Kamata ya yi ta yi aurenta kuma ta ci gaba da karatunta.

Rashin samun na kirki: Samari da ‘yammata da dama sukan fada kaddarar rashin dace. Inda za a ga saurayi ya samu budurwa rumi-rumi, sai tafiya ta yi tafiya a gano ba mutumin kirki ba ne. Wani ma wata manufar ta kawo shi ba auren ba. Daga ya cim ma manufarsa, sai ya kara gaba. Idan kuma ya hadu da yarinyar kirki sai ta kore shi.

Wasu matan suna jin kunyar bayyana wa iyayensu cewa ga abinda ya wakana tsakaninsu da manemansu. Sai kuma ka ga ana zarginta da korar samari.

Lokaci: Wasu kuma suna samun samarin sosai ko ka ga an ja dogon lokaci ana soyayya amma ba a yi aure ba. Wani lokacin auren ne kawai bai yi ba. Daga lokaci ya yi ba makawa za a ga an yi komai an wuce wajen.

Ruwan ido: A gaskiya wasu samarin da ‘yammata suna da ruwan ido da tsananin tsirfa wajen zaben abokin rayuwa. Sai ka ga ‘yar tawaya kadan, ta sa sun fasa auren wani ko wata.  Kowa gani suke bai yi musu yadda suke so ba. Kasancewar dan’adam babu kammalalle marar tawaya, shi ya sa masu wannan ra’ayi suke shan wahala wajen zaben abokin rayuwa.

Amma da za su gano cewa su kansu suna da tawaya irin wacce suke hangowa a jikin wadanda suke fasa aura din, da sun huta wa zukatansu.

Shafar aljanu/ Sihri: Kamar yadda muka sani, shaidanu suna da matukar adwa da aure kuma duk wata hanya da za su bi su ga an wargaza shirin sun hana aure kulluwa, suna yi. Haka akwai shaikanun mutane wadanda kan jefi wata mace ko namiji su hana shi aure. Sai an shirya magana sai ta wargaje. Don haka idan irin wannan matsalar tana yawan faruwa, sai a nemi maganin shafar aljanu da na sihri. Don wani in dai ba a yi ba, sai dai su zauna har abada ba aure.

Daga karshe, ya kamata mutane su sani, fadar wane ya ki aure ko wance ta ki aure tamkar fami kake yi wa zuciyarsu. Kowa yana son ya yi auren nan sai dai idan daya daga cikin dalilan nan ne ya gifta. Bissalam.

Sai mun sake haduwa wani makon da wani sabon maudu’in.

By Editor