Zargin N17bn: Tinubu ya bada umarnin dakatar da binciken da ake yi wa Halima Shehu

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bada umarni kan gaggauta dakatar da binciken da ake yi wa Shugabar shirin NSIPA, Halima Shehu.

Kazalika, Tinubu ya amince da nadin Dokta Akindele Egbuwalo don maye gurbin Halima a matsayin mukaddashi.

Idan za a iya tunawa, ‘yan watanni da suka gabata ne gwamnatin Tinubu ta nada Halima shugabancin NSIPA.

Tun farko, rahotanni sun nuna hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta tsare Halima a Talatar da ta gabata.

An tsare ta ne jim kadan bayan da Shugaba Tinubu ya dakatar da ita daga mukaminta bisa zargin tura kudaden NSIPA Naira biliyan 17 zuwa asusun ajiya a bankin daban-daban a tsakanin mako guda.

Ana zargin Halima da biyan biliyoyin Naira daga asusun NSIPA ba tare da sahalewar Shugaban Kasa ba.

By Editor