Zargin karkatar da N585m:  Tinubu ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike kan Betta Edu

Spread the love

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya ba da umarnin a binciki Ministan Jinkai da Yaki da Talauci, Dokta Betta Edu, dangane da karkatar da Naira miliyan 585 da aka ware don ba da tallafin rage radadin rayuwa zuwa wani kebabben asusu.

Bayanin haka na kunshe ne cikin sanarwar da Ministan Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya fitar a ranar Lahadi.

A cewar Idris, “Gwamnatin Tarayya, karkashin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, na aiki ne da gaskiya ga jama’a tare da tabbatar da an zuba kudaden gwamnati a inda ya dace don magance matsalolin bukatun ‘yan Nijeriya.

“Duba da abubuwan da suka faru a baya-bayan nan, Shugaban Kasar ya ba da umarni kan a gudanar da cikakken bincike domin tabbatar da sahihancin bayanan da aka gabatar,”

Sanarwar ta kuma ja hankalin jama’a kan a yi hattara da rahotannin da ake yadawa a intanet kan wannan batu, sannan su dogara da Ma’aikatar Yada Labarai da Wayar da Kai karkashin jagorancin Minista Mohammed Idris, domin samun sahihan bayanai game da harkokin Gwamnatin Tarayyar Nijeriya.

By Editor