Gwamnan Zamfara ya sha alwashin  ɗabbaƙa kasafin 2024

Spread the love

Gwamnan Jihar Zamfara,  Dauda Lawal, ya sha alwashin aiwatar da kasafin gwamnatinsa a 2024 don amfanin jihar da al’ummarta.

Lawal ya sha alwashin haka ne yayin da yake jawabi a wajen taron Majalisar Zartarwa da ya gudana ranar Litinin karkashin jagorancinsa a Fadar Gwamnatin Jihar da ke Gusau, babban birnin jihar.

Mai magana da yawun Gwamna Lawal, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa, taron majalisar ya tattauna muhimman batutuwan da suka shafi jihar, ciki har da batun kasafin jihar na 2024.

Sa’ilin da yake jawabi, Gwamna Lawal, ya jaddada zai yi amfani da ingantattun tsare-tsaren da ke kunshe cikin kasafin na 2024 mai taken ‘Kasafin Ceto’ domin cimma nasara.

Ya ce, “Idan muka waiwaya baya, yana da muhimmanci mu yi godiya da irin nasarorin da wannan gwamnati ta samu duk da kalubalen tattalin arziki da walwalar rayuwa.

“A gaskiya, kokarinmu, ya haifar da sabuwar ajanda ga sha’anin shugabanci a jihar. Labarin Jihar Zamfara ya canza a tsakanin watanni bakwai da suka gabata, kuma jihar na samun cigaba a daukacin bangarori,” in ji Lawal.

Ya kara da cewa, a lokacin da suka kama mulki ran 29 ga Mayun 2023, sun ayyana muhimman bangarori tare da da ba da muhimmanci wajen magance matsalolin da suka fi addabar al’ummar jihar.

Kazalika, ya ce gwamnatinsa ta samar da shirye-shirye da da tsare-tsare masu inganci domin cimma manufar kasafin 2024 a fadin jihar.

By Editor