Tare da ABBA ABUBAKAR YAKUBU
Halin kuncin rayuwa da yunwa da ake fama da shi a wannan lokaci na koma bayan tattalin arziki da talauci a kasa, ya jefa iyalai da magidanta da dama cikin wani mawuyacin rayuwa.
Samun damar cin abinci sau uku ko sau biyu a wuni ya fara zama tarihi a wajen wasu. Magidanta da dama sun zama marokan karfi da yaji, tun mutum na jin nauyin ya yi roko, har ya fara zama masa jiki, don dai neman abin da zai ciyar da iyali, ko da kuwa shi zai hakura ya kwana da yunwa.
Muna sane da cewa, babu wani dan Nijeriya da wannan tsananin bai taba ba, sai dai tsiraru wadanda Allah ya tarfawa garinsu nono! Hatta masu arziki da rufin asiri da muke musu kallon su ne dama-dama to, su ma yanzu kuka suke yi. Koda ba don sun rasa gabadaya ba, don irin yadda nauyin ’yan’uwa da abokan da aka taso tare ke kara hawa kansu. Sannan abin da aka saba samu a baya yanzu ya fara raguwa ba kamar da ba.
Abin tausayi ne yadda za ka ga mutumin da a baya yake da rufin asiri, amma yanzu talauci ya sarkafe shi, da kyar ake samun abin da za a ci a gidansa. Idan kana son ka ga zahirin hakan kai ziyara gidan wani abokinka karamin ma’aikaci, ko dan kasuwa mai qaramin jari, ko wanda ke ci a karkashin wani da shi ma harkokinsa suka fara ja da baya.
Ko kuma ka leka makwafta irin gidajen da maigidan ke kwance yana fama da jinya ba ya iya fita aiki ko kasuwa, kuma masu dan tallafa musu sun fara gajiya, ga akasarin yaransa kanana ne. Ko iyalin da maigidan ya rasu ya bar yara marayu da mata biyu ko uku suna zaune babu tabbas din samun abin da za su ci yau ko gobe.
Irin wadannan mutane idan ka gansu a titi sun fito suna roko, ko suna bibiyar ’yan uwa da abokan arziki, don a tallafa musu da abin da za su ci, bai kamata a tsangwame su ko kyare su ba. Ko ba ka da abin da za ka bai wa mutum kada ka wulakanta shi ko ka muzanta shi don ya roki abin da zai ci. Ba kowa ne ke jin dadin roko ba, kuma ba kowa ne ya zama dan maula ko dan kala kamar yadda wasu ke fada ba. Alqur’ani mai girma ya fada mana cewa, kada ku kyari masu zuwa rokonku!
Kodayake ana samun wasu baragurbin mutane da suka mayar da roko ya zama sana’arsu, ba sa aikin komai sai dai bibiyar abokai da makwafta ko masu hali suna rokonsu basu kudi, don biyan wata bukata da ta takura su, musamman a kafafen sada zumunta ko ta waya. Amma hakan ba dalili ne da zai sa duk wani magidanci ko mai karamin karfi da ya zo maka da bukata ya zama cima-zaune ba.
Ko da kuwa a baya ka san shi a matsayin mutum mai rufin asiri, ba abin mamaki ba ne a yanzu ya samu kansa cikin jarabawar rayuwa, ko karayar tattalin arziki, wanda yana iya faruwa da kowa. Idan ka ga ya samu kansa cikin masu rokon abin da za su ci kada ka kyamace shi, ko ka sa shi a gaba kana gulmarsa da aibata shi a cikin mutane. Gobe kai ma Allah yana iya jarabtarka, kuma ya zama shi ne ke da damar taimaka maka.
Duk da kasancewar addinin Musulunci da mutuntaka ta dan Adam ba su lamuncewa mutane su zama maroka ba, amma roko na iya zama dole ne a yanayin da mutane suka rasa madafa ko aka shiga cikin annoba da kangin yanayin da ya shafi kowa. Don haka ya kamata a rika yi wa mutane uzuri, a halin da ake ciki, kada a aibata su ana nuna basu da juriyar babu, ko ba su da tawakkali da sauransu.
Yunwa fa bata san wannan ba, duk dauriyar mutum akwai inda yake da rauni, kuma raunin wani ba illa ba ce, lalura ce! Babu ma kamar idan batun iyali ya gifta, don kuwa duk wani magidanci nagari da ya san inda ke masa ciwo, ba zai taba kwantar da hankalinsa ba, idan iyalinsa na zaune cikin yunwa da quncin rayuwa.
A irin wannan yanayin ne da ake hantarar masu rokon abin da za su ciyar da iyalinsu, ake samun wasu masu raunin suna aikata wasu abubuwa da basu kamata ba, kamar irin su sata da bin maza, wadanda ba za su bai wa mace taimako ba, sai in za ta ba da kanta garesu.
Wasu vata-gari na amfani da wannan yanayin da ake ciki suna bata ‘ya’yan mutane da matan wasu, don ganin halin da suke ciki, suna yi musu tayin samun taimako daga gare su idan su ma za su amince su taimaka musu, wato su yarda a yi fasikanci da su. Wa’iyazubillahi!!
A irin wannan lokaci ne, ake samun karuwar mace-macen magidanta, sakamakon lalurori masu nasaba da hawan jini da bugun zuciya, saboda yawan tunani, tsoro, da firgici kan halin da su da iyalinsu ke ciki. Mutane da dama masu kyan sura da kwarjini sun lalace sun fita hayyacinsu, saboda yunwa da kuncin rayuwa da suka samu kansu a ciki. Wasu tun tasowarsu ba su taba ganin jarabawar rayuwa irin wannan da ake ciki a yanzu ba.
Kwanaki na ga wani labari da ake yadawa a zaurukan sada zumunta da ke nuna cewa wata mata a Jihar Kaduna ta dafa ruwan zafi ta sa gishiri a ciki ta bai wa yaranta, saboda da rashin abin da za ta ba su su ci.
A dalilin haka kuma suka rasa ransu, har hakan ya haifar da zanga-zangar mata a cikin garin saboda nuna damuwa da halin da ake ciki. Labarin mutanen da ke rataye kansu su mutu, don rasa mafita a rayuwarsu, ya daina zama abin mamaki, sakamakon yadda ya fara zama ruwan dare.
Har zuwa yaushe za a cigaba da irin wannan rayuwa? Muna samun labarin yadda ’yan siyasa da jami’an gwamnati ke cewa suna iyaka kokarinsu don shawo kan lamarin, da yadda ake cewa gwamnati za ta bude iyakokin kasa don shigo da wasu nau’ikan kayan masarufi, don rage radadin da talakawa ke ciki. Amma shin hakan ya wadatar kuwa? Lallai akwai bukatar gwamnati ta fitar da wasu sabbin dabaru da tsare-tsare da za su kawo sauyi na musamman a rayuwar ’yan kasa. Don gaskiya ana ji a jiki, jama’a na wahala sosai.
Sannan kamar yadda muka saba fada a wannan shafi, ba zai yiwu jama’a su cigaba da nade hannu suna jiran taimako daga gwamnati ko wasu ’yan siyasa, su shiga neman karin hanyoyi da dabarun neman sana’o’i da abin dogaro da kai. A irin wannan lokaci ne ake neman sana’a goma, da ake ce maganin mai gasa, domin idan ba a dace a nan ba za a dace a can, kuma a rika hakuri da karamar riba.
Sannan a vangaren iyali a riqa taimakawa juna ana tallafawa da abin da ba zai gagara ba, don a rufawa kai asiri. A rage dorawa kai nauyin da bai zama tilas ba, kuma a koyi kawar da kai daga wasu abubuwan da ke faruwa a dalilin rashi ko talauci, sabanin yadda aka saba gani a baya. Ba lallai ne nishadi da jin dadin da ake samu a shekarun baya su dore ba, har sai abubuwa sun daidaita.
Malamai da sauran ’yan kasa su qara himmatuwa da addu’o’i da azumi don neman taimakon ubangiji, da samun sassauci a halin da ake ciki. Mu rika taimakawa marayu da masu karamin karfi da ke tare da mu, idan Allah Ya hore mana. Kada mu rika hantarar marasa shi, ko tsangwamar masu rokon mu taimaka musu. Mu rufawa kai asiri, mu tallafawa juna, mu kuma nemi taimakon ubangiji kan duk abubuwan da ke faruwa da rayuwarmu!
