’Yan bindiga sun sake kashe dagaci da mutum 10 a Katsina 

Spread the love

Daga UMAR GARBA a Katsina

’Yan bindinga sun kashe mutane 10 ciki har da Maigari a kauyen Kukar Babangida da ke Karamar Hukumar Jibiya a Jihar Katsina.

Shugaban Karamar Hukumar Bishir Sabi’u, ya tabbatar wa DW Hausa kashe mutanen, inda ya ce ‘yan bindingar sun shiga kauyan ne da misalin karfe daya da rabi na daren ranar wannan Alhamis din.

‘Yan bindigar na ci gaba da kashe mutanen da ba su ji ba su gani a wasu daga cikin kauyukan kananan hukumomin jihar duk da kokarin da jami’an tsaro da ma gwamnatin jihar ke cewa suna yi don dakile matsalar.

Ko da a makon da ya gabata Blueprint Manhaja ta rawaito cewar, ‘yan bindigar sun tare wani ayarin motocin ‘yan kasuwa a garin ‘Yan Tumaki na karamar hukumar Danmusa, inda suka kashe mutane takwas tare da jikkata wasu daga cikin Jami’an tsaron dake yi wa motacin rakiya zuwa cin kasuwar mako-mako.

By Editor