Edu ba ta cinye Baitulmali du ba

Spread the love

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Batun almundahana a Nijeriya ai ba sabon abu ba ne don kama daga lokacin mulkin soja har dawowa farar hula da a ke ciki yanzu daga 1999, kalubalen ya zama ruwan dare a Nijeriya. A baya an dau abun ba wani babba ba ne da ya wuce wasu baragurbi a jami’an ‘yan sanda da kan karbi kudi ‘yan kalilan daga direbobi a kan tituna don kyale su su wuce ba tare da wani bincike ba.

Hakanan in mutum na son a bar shi ya ketare wani shinge da ba shi da hurumi sai ya riqe abun da a ke kira na goro don a bude ma sa kofa ya wuce. Wani abun kuma ya shafi makarantu inda wasu dalibai da ba sa son karatu kan ba da cin hanci don a ba su dama su yi satar jarrabawa ko kuma a ba su maki ba tare da sun yi wani kokarin amsa tambayar jarrabawa ba.

Kazalika a kan samu har yanzu wasu manyan laifuka da a kan kama wasu malaman jami’a da na wasu manyan makarantu na neman cin zarfin dalibai mata don ba su dama su yi nasara a jarrawaba ko yi mu su barazana cewa ta mummunar hanyar ce kawai za su iya samun sakamakon jarrabawa mai kyau.

A nan ya nuna hanyar cin hanci da rashawa na da yawa kuma duk a karshe a kan yi karantsaye ga doka. In za a yi wa mai bayra da cin hanci da mai karva kudin goro cewa duk masu laifi ne, za a iya uzuri da yadda wasu matasa kan kammala makaranta amma sai aikin gwamnati ya gagara sai sun ba da kudi kafin a ba su dama. Ina ga wasu alkalai masu zarmiya ina ga bata-gari a tsakanin jami’an zabe da sauran su.

Wannan fa matsalar ta shiga har cikin wasu da kan canki sabon Sarki inda mai hannu da shuni kan yi nasara kan sauran amsu nema ko da kuwa bai cancanta ba. Ta’azzarar lamuran almundahana na kassara cigaban kowace kasa da ta samun kan ta a wannan yanayi. Duk wata nasara ta kan samu cikas don illar cin hanci ta yadda wadanda ba su cancanta ba kan dare kan madafu su yi ta aikata ayyukan da hankali ma ba zai dauka ba.

Misali a yayin da a ka bar wani dan takarar neman kujerar siyasa ya kashe makudan kudin sa a kamfen ta hanyar sayen masu kada kuri’a, to zai yi wuya ya tabuka abun kirki gabanin maida gurbin kudin da ya kashe da samun ribar ribau. Ga yanda lamarin kan auku a Nijeriya masu sharhi kan ce kasar na da tarin dukiya ne ta yadda za a yi ta sata amma kuma a bar sauran dukiya.

Sashen nazarin nan ka iya zama daidai ne amma sashe akwai kuskure don ko akwai dukiyar, illar da hakan kan haifar da kan jefa wasu cikin qunci har ya kai ga wasu su rasa ran sa zai nuna illar satar na nan ko da dukiyar ba ta karewa. Ai shi ya sa a ke cewa ina ribar badi ba rai.

Kuma abun takaicin shi ne wasu daga cikin masu sace dukiyar kan ktara da ita can kasashen turai su jibge a wasu bankunan da kudin na iya salwanta. Wasu kuam za su yi ta tara dukiyar ba tare da sun amfani kan su ba balle wani. An gano akwai wasu gidaje a manyan birane irin Abuja da a ka saye shi da kudn haram ko kuma a ce don dabarar boye kudin haram. Akwai labarin wani da a ka taba zargi ya mallaki manyan gidaje a Abuja ya aiyana wasu gidajen da cewa ba ma nasa ba ne don gujewa zurfin tuhuma.

Wani abun damuwa shi ne yadda a kan samu wasu jami’an yaki da cin hanci da zarmewa. Zai zama babban abun damuwa a nada jami’i ya yi aiki a hukumar tabbatar da gaskiya da amana, sai a zo a tarar an ci amanar. Hakika hakan kan jefa ayar tambaya shin gwamnati ce ba ta da gaskiya ko rashin sa’ar nada jami’an ne?

Tsohuwar gwamnatin Buhari ta fito karara ta zargi tsohon mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci Ibrahim Magu da laifin sace abun da hukumar ta kwato daga varayin biro inda hakan bai tabbata a gaban kotu ba kuma bayanai daga baya na nuna lamura masu rikitarwa don yadda wanda a ka nada ya gaji kujerar Magu wato Abdulrasheed Bawa shi ma hukumar ‘yan sandan farin kaya ta yi awun gaba da shi na tsawon lokaci don shan tuhuma.

Kafin mu zayyana bayanan da su ka biyo bayan dakatar da ministar ma’aikatar jinkai Betta Edu da ya zama babban labari a makon nan za mu duba yanda bincike ya fada kan wasu kamfanoni da a ke hasashen sun amfana daga canjin dala ta barauniyar hanya da hakan babbar hanay ce ta cin hanci da rashawa. Kamfanin kasuwancin nan na Dangote ya bayyana cewa ya na ba da duk hadin kan da hukumar EFCC ke buqata wajen binciken karvar dala a canjin gwamnati daga babban bankin Nijeriya.

In za a tuna EFCC ta buqaci cikekken bayanin yadda kamfanin ya karbi canji mai rangwame na gwamnati daga 2014 zuwa bana.

Kamfanin Dangote ya kara da cewa, ya san ba shi kadai a ka bukaci ya ba da irin wannan bayanin ba.

Duk da haka kamfanin ya nuna damuwa cewa lokacin da wakilan sa ke hukumar EFCC da takardun bayanai da a ke bukata, EFCC ta qi karvar takardun inda a lokaci guda ta tura jami’an ta don neman takardun kai tsaye daga helkwatar kamfanin a Lagos.

Kamfanin Dangote ya nuna bai sava wata doka kan karvar canjin ba kuma ya na da bayanan duk abun da EFCC ke bukata.

An sha zargin babban banki da azurta wasu kamfanoni da daidaikun mutane da ba su canjin dala bisa farashin gwamnati da hakan ya yi ta aukuwa zamanin mulkin tsohon shugaba Buhari.

Babban bankin Nijeriya CBN ya kori ‘yan majalisar gudanarwa na wasu bankuna 3 da a ke bincike a kan su.

Bankunan da lamarin ya shafa cikin sanarwa daga CBN sun hada da Keystone, Polaris da Union.

Ba mamaki hakan ya zama ya na daga cikin shawari da babban mai binciken aiyukan babban banki da shugaba Tinubu ya nada wato Jim Obazee ya bayar bayan zargin tsohon shugaban babban banki Godwin Emefiele da mallakar wasu daga bankuna ta hanyar kudin almundahana.

Obazee wanda ya gayyaci masu hannun jari na bankin TITAN da su ka sayi bankin Union da Keystone; ya yi gargadin rashin zuwan su zai iya sa su sarayar da hannun jarin na su ga gwamnati.

Ministar ma’aikatar jinqai ta Nijeriya Betta Edu na shan caccakar tura zunzurutun kudi Naira miliyan 585.2 daga asusun sashen tallafi na ma’aikatar ta zuwa ma’ajiyar wata ma’aikaciya Bridget Mojisola.

A takardar bukatar a tura kudin daga ofishin babbar akanta Oluwatosin Madein da a ka yi kwarmaton ta, ministar ta ce za a tura kudin ne wajen wasu talakawa a wasu jihohi.

Edu wacce ta ce halal ne tura kudi zuwa ga asusun ma’aikaciya, ta kare hakan da cewa Bridget akantar shirin tura tallafin ne.

Babbar akanta Madein ta nesanta kan ta daga bukatar, ta na mai cewa an shawarci Edu kan qa’idar doka ta yadda za a tura kudin da ya dace a tura su kai tsaye ga ma’ajiyun banki na wadanda za su ci gajiya.

Wannan na nuna Edu na cikin zargin yiwuwar tafka badakala don ba ta saurari shawarar babbar akantar kasa ba inda ta tura kudin ga ma’ajiyar Birdget ta bankin UBA. Wannan ya sa shugaba Tinubu daukar matakin dakatar da Edu da umurnin hukumar EFCC ta gudanar da bincike don gano hakikanin abun da ya faru.

Jim kadan bayan dakatar da ita daga aiki bisa tuhumar yiwuwar badakalar sama da Naira miliyan 565; jami’an fadar Aso Rock sun hana dakatacciyar ministar ta jinkai Betta Edu ganawa da shugaba Tinubu.

Ba mammaki ministar na yunqurin ganawa da shugaba Tinubu ne don yi ma sa bayanin halin caccaka da ta ke ciki tun bayyanar labarin umurnin ta na a tura miliyoyin Naira ma’ajiyar bankin wata akanta.

An ga motar da ke dauke da Edu na ficewa daga fadar Aaso Rock don rashin nasarar samun damar shiga wajen shugaban.

A yanzu haka Edu na fuskantar bincike daga hukumar EFCC bayan ta mika ragama ga babban sakataren ma’aikatar. Bayan labarin titsiyewa a EFCC an ba da belin Edu ta dawo gida.

Kammalawa;

Hakika akwai abun dubawa a Nijeriya inda bincike kan kare daga ba da beli ko dakatarwa. Abun da ya fi dacewa shi ne a fito da bayanai dalla-dalla a bayyanawa jama’ar kasa sakamakon bincike don gano mai laifi ko wanda ba shi da laifi. Alamu na nuna ko dai ba a dau wani hukunci kan Edu ba, zai yi wuya ta koma kujerar minista in an duba tsarin matakan gwamnatin Nijeriya. Abun da ke daukar hankalin mutane shi ne jerin mata da ke karuwa cikin tuhumar cin hanci. Wannan ya ci karo da tunanin mata kan iya zama masu amana fiye da maza.

A takaice dai duk kanwar masu almundahana ja ce tsakanin maza da mata, matasa da tsoffi. Duk satar da a ka yi a Nijeriya a kan yi tunanin ba za a iya kwashe dukiyar DU BA!

By Editor