Daga BASHIR ISAH
Al’ummar garin Ibadan, babban birnin Jihar Oyo sun gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna rashin jin daɗinsu dangane da matsalar tsaron da ke ci wa ƙasa tuwo a ƙwarya da kuma tsadar rayuwar da ‘yan ƙasa ke fama da ita.
Don haka masu zanga-zangar suka yi kira ga Shugaban Ƙasa Bola Tinubu kan ya magance waɗannan matsaloli domin walwalar ‘yan ƙasa.
Masu zanga-zangar waɗanda galibinsu matasa ne, sun ce sun karaya da irin halin da ƙasa ke ciki, don haka suke buƙatar gwamnati ta ɗauki ingantattun matakai domin gyara.
An ga matasan ɗauke da kwalaye masu ɗauke da saƙonni daban-daban da suka haɗa da: “Dole Tinubu ya magance matsalar tsaro” da “Yunwa na kashe mu” da sauransu.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Nijeriya ke fuskantar ƙalubalan tsaro da suka haɗa da hare-haren ta’addanci, garkuwa da mutane da sauransu.
Duk da dai zanga-zangar ta lumana ce, amma an ji tsoron kada hakan ya rikiɗe ya haifar da akasi muddin gwamnati ba ta fito ta saurari jama’a ba.
