Tinubu da Atiku sun yi musayar yawu kan taɓarɓarewar tattalin arziki

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Fadar shugaban ƙasa da kuma tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar sun yi ta cacar baki mai zafi game da manufofin tattalin arzikin gwamnatin tarayya, musamman faɗuwar darajar Naira.

Tsohon mataimakin shugaban Nijeriyan ya yi doguwar magana a shafinsa na X a ranar Lahadi, inda ya zargi Bola Tinubu da jefa tattali a matsala.

Atiku Abubakar yana ganin kura-kuren gwamnatin Tinubu sun gurgunta tattalin arzikin Nijeriya, wanda hakan ya jawo tashin da Dala ta ke yi.

A jawabinsa, Atiku wanda ya zo na biyu a zaɓen 2023 ya ce, kyau a canja irin salon da ake ɗauka wajen magance halin da ƙasar ke ciki.

Atiku Abubakar ya ce, “A zaman da aka yi na ranar Alhamis domin magance matsalolin kuɗin ƙasar waje da matsalar rushewar tattalin arziki da sauransu, Bola Tinubu ya sake nuna gwamnatinsa ba ta da wasu kwararan tsare-tsare domin shawo kan matsalolin hauhawan kuɗi da talauci da ƙasar ta k fuskanta.”

“A maimakon haka sai ya faɗawa ƙasar cewa a daina kauda hankalin masanan da ke bada shawarar yadda za a shawo kan matsalar kuma a ba su lokaci domin cigaba da bushasharsu da ta jefa ƙasar a matsala,” inji Atiku.

Wazirin Adamawa ya ce, ba za su yi shiru a riƙa wahalar da mutane da tsare-tsaren APC ba.

Amma da take mayar da martani kan kalaman Atiku a daren Litinin, fadar shugaban ƙasa a cikin wata sanarwa mai taken, ‘Tsohon mataimakin shugaban qasa Atiku Abubakar ya sake tafka kuskure’, mai ɗauke da sa hannun Bayo Onanuga, ta ce, “Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar, a ƙoƙarinsa na lalata tsarin yadda gwamnatin Tinubu ke tafiyar da tattalin arzikin ba zai yi nasara ba.”

“Haka zalika, ya kasa faɗin gaskiya ga sabon tsarin da Gwamna Olayemi Cardoso da tawagarsa ke aiwatarwa a babban bankin Nijeriya.

“Da farko dai, ba gaskiya ba ne cewa ganawar da shugaba Tinubu ya yi a ranar Alhamis da ta gabata da gwamnonin jihohi 36 ya ta’allaƙa ne kan batun rikicin canjin kuɗaɗen ƙasashen waje da kuma canjin kuɗi.

A cewar sanarwar, shawarwarin da aka yanke a taron sun nuna muhimman batutuwan da aka tattauna: Za a ƙarfafa masu gandun daji da makamai, yayin da ’yan sanda za su ɗauki ƙarin ma’aikata da kuma majalisar tattalin arzikin ƙasa domin zurfafa tattaunawa kan samar da ’yan sandan jihohi.

Ta kuma bayyana cewa, shugaba Tinubu ya tabbatar da amincewarsa na fitar da ton 42,000 na hatsi daga asusun ajiyar ƙasar.

A halin da ake ciki dai, duk da ƙoƙarin da babban bankin Nijeriya (CBN) ya yi na dawo da hayyacinta a kasuwar canji ta hanyar fitar da wasu sabbin da’ira har guda uku, Naira ta kara fuskantar faɗuwa a ƙarshen mako.

Naira ta sake samun koma baya a kasuwannin canji a hukumance da kuma na ɗaiɗaikunta a ranar Juma’a.

By Editor