Ƙudirina shi ne inganta Hukumar Kula da Ilimin Kimiyya da Fasaha a Kano – Farfesa Ɗahiru Saleh

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJJITABA a Kano

Shugaban Hukumar Kula da Ilimin Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kano, Farfesa Ɗahiru Saleh Muhammad, ya bayyana cewa babban burinsa shi ne inganta ayyukan hukumar kimiyya da fasaha ta Jihar Kano a mastayinsa na masani akan harkar ilimin kimiyya da fasaha.

Don haka ya ce ƙudirinsa shi ne ɗaukaka darajar hukumar da kuma yin aiki bisa ƙa’idar koyar da ilimin kimiyya da fasaha domin kwalliya ta biya kuɗin sabulu wato kowacce ƙwarya a ajiyeta a gurbinta, kamar yadda ƙudirin gwamnan Kano ya ke Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ke na bunƙasa ilimin kimiyya da fasaha da ma ilimi baki ɗaya, wanda a cewarsa shi ne gwamna na farko a ƙasar nan da ya ware kashi 30 cikin 100 a kasafin kuɗinsa na 2023 zuwa 2024.

Farfesa Ɗahiru Sale, ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a ranar Juma’a da ta gabata a ofishinsa dake birnin Kano.

Har ila yau Farfesa Ɗahiru Saleh Muhammad, wanda ke tare da Malam Mahadi Shugaban Ma’aikata na hukumar, a lokacin hirarsa da ‘yan jarida ya bayyana cewa tun farkon zuwansa hukumar ya ziyarci makarantu da ke ƙarƙashin hukumar inda ya samu wasu matsaloli a wasu makarantu wanda nan take ta ɗau mataki na ganin komai ya tafi daidai bisa ƙa’ida kuma shi ne abin ya sa gaba a halin yanzu.

Daga cikin sabbin tsare-tsaren da ya zo da su akwai shirya jarrabawa bai ɗaya da wasu makarantu 22 cikin 44 da tsohon gwamnan Kano Sanata Eng Rabiu Musa Kwankwaso, ya kammala 22 a zuwansa na 2011 zuwa 2015 to waɗanda ya kammala saboda siyasa da a ba su muhinmanci ba ba da su ake jarrabawa ba an dai bar su ne jeka na yi ka kuma kayan koyarwa da aka kai makarantun duk an ajiyesu ba a aiki da su to yanzu na kafa kwamitin bincikosu da kuma yadda za ai aiki dasu domun inganta ilimin kimiya da fasaha a jihar Kano.

Haka kuma wani abun takaici da na ƙudiri gyaransa shi ne zakaga akwai waxanda ba masu ilimi ko kwarewa a kan fannin kimiyya da fasaha ba amma su na koyarwa ko ma suna shugabantar makarantun wanda wannan kuskure ne da na ƙudiri gyara shi a wannan hukuma ta kula da ilimin kimiyya da fasaha ta jihar Kano da ikon Allah.

Haka zalika yanzu haka hukumar kula da ilimin kimiyya da fasaha da Jihar Kano na tsare-tsare na shirya jarrabawa mai inganci ta hanyar wanda ya samu cin jarabawa kuma aka gwada shi bayan jarabawar to shi ne zai zama ya samu shiga makarantun kimiya da fasaha na jihar Kano kuma akwai tsari na gayyato ƙwararru a fanin kimiyya da fasaha na wajen hukumar da kuma ƙwararru da Allah ya albarkaci hukumar kula da ilimun kimiya da fasaha ta jihar Kano da su to waɗanan ƙwararru su ne za su zauna su tantance ɗalibai bayan sun yi jarrabawa domin tabbatar da cewa waɗanda suka ci ne kawai za a ɗauka a wannan fanni na koyar da ilimin kimiyya da fasaha a jihar kano.

A ƙarshe ya yi alƙawarin haɗa kai da ɗaukacin ma’aikatan hukumar kula da ilimin kimiyya da fasaha da kuma tabbatar da jin daɗinsu da walwalarsu dai dai da manufar Gwamna Abba Kabir, ta kyautatawa ma’aikata da ɗaukacin al’ummar Kano.

By Editor