Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Mataimakin shugaban amajalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya ce suna da ƙuduri na ganin sun haɗa kan ƙungiyar ECOWAS.
Ya ce, “Kafin zuwan Turawa, ƙasashen Afirka ta Yamma ko ECOWAS sun kasance ƙasa ɗaya. Ana yin Hausa a kowane yanki ka je kama daga Nijar, Mali, Ghana da sauransu haka ma ga duka sauran yaruka”.
Barau ya bayyana haka ne yayin tattaunawa da BBC, inda ya ce ya zama wajibi ECOWAS ta haɗa kai domin samun ci gaban da ya kamata.
“Bayan zuwan Turawa ne suka raba kawunanmu, kuma ya kamata mu haɗa kai yanzu,” in ji Barau.
Ya ce idan an haɗe za a fi samun cigaba da walwala da kuma jin daɗi na al’umma.
Mataimakin shugaban majalisar ta dattawan, wanda shi ne kakakin riƙo na majalisar ta ECOWAS, ya ce za su yi duk abin da za su iya wajen haɗa kan mambobin ECOWAS.

Ya kuma ce suna da ƙudurin ganin an samar da kuɗi na bai-ɗaya na ƙasashen.
Barau ya ce suna da ƙudurin kawo tsarin da zai kawo haɗin kai ta hanyar tattalin arziki da tsaro da kuma cigaban yankin.
