Hajjin 2024: Tinubu ya tallafa wa maniyyata da Biliyan N90

Spread the love

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Mataimakin Shugaban Nijeriya, Kashim Shettima, ya bayyana cewa, gwamnatin Shugaba Bola Tinubu ta tallafa wa maniyyatan aikin hajjin 2024 da Naira Biliyan 90.

Shettima ya bayyana haka ne ranar Laraba a wajen ƙaddamar da fara tashin maniyyatan aikin Hajji na ƙasa na shekarar 2024, wanda aka gudanar a filin jirgin saman Sir Ahmadu Bello International Airport da ke Birnin Kebbi.

“Za ku iya tuna cewa, a bana mun fuskanci babban ƙalubale wajen bayyana gundarin adadin kuɗin aikin hajjin 2024, sakamakon yadda farashin canjin kuɗin qasashen waje ya tashi.

“Don haka Shugaba Bola Tinubu ya yi aiki ba dare ba rana, domin shawo kan koma-bayan da kuɗinmu na gida ke yi, domin kawo sauƙi ga maniyyatanmu da sauran ’yan Nijeriya.

“A ƙarshe matakin ya yi nasarar rage kuɗin aikin hajjin. Shugaban ƙasar ya amince da fitar da Naira Biliyan 90, don bayar da tallafi na aikin hajjin bana.”

Ya kuma ce, gwamnatin ta sake fasalin Nijeriya ƙarƙashin jagorancin Tinubu, inda ta ke bai wa aikin addini muhimmanci, saboda irin rawar da ya ke takawa wajen sauya halayya da zamantakewar muminai a ƙasar.

“Saboda wannan babban al’amari, gwamnati ta ɗauki lokaci a hankali wajen zaɓo mutane masu gaskiya da sanin makamar aiki da kuma sadaukar da kai, don tafiyar da al’amuran hukumar hajji ta Nijeriya, domin amfanin alhazan Nijeriya.

“Gwamnati na kula da duk shirye-shiryen da ake yi na kyautata rayuwar alhazanmu a Saudiyya da kuma cikin ƙasar kafin su tafi.

“Mu na sane da tanadin da aka yi don kare lafiya, tsaro da jin daɗin tawagar maniyyatan Nijeriya zuwa aikin hajjin 2024 na mahajjatanmu.”

Daga nan sai Shettima ya buqaci alhazan Nijeriya su jajirce wajen yi wa gwamnatin Tinubu addu’ar samun nasara, zaman lafiya da cigaban qasa, wanda hakan zai sa a yi alfahari da ƙiran ƙasarmu ta “uwa.”

“Haƙiƙa, ta hanyar addu’o’inmu da kuma gudunmawar ɗaiɗaiku ne ƙasarmu za ta cigaba,” inji Shettima.

Tun da farko, Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar III, ya ɗora wa maniyyatan Nijeriya alhakin nuna halin ƙwarai, domin su fito da martabar Nijeriya yadda ya kamata.

Ya kuma gode wa Tinubu kan jagoranci Gwamnatin Tarayya bisa ƙoƙarin da ta ke yi na ganin an gudanar da aikin hajjin 2024.

“Kamar yadda ku ka ji cewa, Shugaban Hukumar NAHCON ya ce a lokacin da duk a ka samu wani koma-baya, haske ya bayyana a gefe ɗaya kuma, a yau mun fara jigilar Hajjin bana na 2024.

“Ba mu tava yanke fatan za mu je aikin hajji ba. Mu na cikin zamanin Sabunta Nijeriya. Don haka ku gaya wa Asiwaju cewa, har yanzu ana sa ran fatansa na haƙiƙa ya haskaka ko’ina.

“Mu na neman kari, mu na son ƙarin jagoranci nagari. Mu na so mu gode wa Shugaban Ƙasa bisa jagorancinsa.

“Mu na godiya ga Mataimakin Shugaban Ƙasa da dukkan gwamnonin jihohinmu, waɗanda su ka tsaya tsayin-daka, don taimaka wa talaka ya tsira.”

Hukumar NAHCON ta bayyana cewa, za a kammala jigilar dukkan maniyyatan da za su tashi daga Nijeriya zuwa ƙasar Saudiya, domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2024 a ranar 10 ga watan Yuni ko kuma kafin ranar.

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa, aqalla maniyyatan Nijeriya 50,000 ne za su yi aikin Hajjin shekarar 2024 a ƙasar Saudiyya.

Blueprint Manhaja ta ruwaito cewa, Ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta ware wa Nijeriya gurbi guda 95,000, domin gudanar da aikin hajjin shekarar 2024, amma ’yan Nijeriya ba su iya cike gurbin ba, saboda abinda a ke danganta wa da halin matsin rayuwa, wanda ya haɗa da tashin gwauron zabin da Dala ta yi a kasuwar shunku ta duniya da faɗuwar da Naira ta yi.

By Editor