Badaƙalar Sarauta: Za mu bi umarnin Kotu wajen hana maido da Sanusi a matsayin Sarkin Kano — ‘Yan Sanda

Spread the love

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta lashi takobin yi wa umarnin kotu biyayya wajen dakatar da naɗa Muhammadu Sunusi II a natsayin Sarkin Kano, da kuma hana Gwamnatin Jihar rushe sabbin masarautu biyar da aka ƙirƙiro a jihar.

Kwamishinan’Yan Sandan Jihar, Muhammad Hussain Gumel ne ya bayyana hakan ga manema labarai a ranar Asabar a Babban Ofishin Rundunar da ke Bompai, Kano.

Ya ce, “Za mu yi biyayya ga umarnin Kotu na bar komai yadda yake har sai kotu ta yanke hukunci.”

A ranar Alhamis ne dai Babbar Kotun Tarayya da ke Kano ta ba da umarnin wucin-gadi na hana gwamnatin jihar maido da Sanusi II a matsayin Sarkin Kano.

Umarnin na Kotu, ya biyo bayan ƙarar da Alhaji Aminu Bappa Dan Agundi ya shigar ne inda yake ƙalubalantar gyaran fuskar da Majalisar Dokokin Kano ta yi wa Dokar Masarautun Kano.

Alƙalin Kotun, Mai Shari’a A.M. Liman, shi ne ya ba da umarnin, inda ya buƙaci da a dakatar da aiwatar da dokar da aka yi wa kwaskwarima wadda tuni Gwamman Kano, Abba Kabir Yusuf ya rattaɓa hannu.

By Editor