DSS ta gargaɗi masu zanga-zangar ‘June 12’

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

An gargaɗi mutane da su ƙauracewa dukkan nau’o’in zanga-zanga da ka iya haifar da tashin-tashina a tsakanin al’umma yayin gudanar da shagulan bikin murnar ranar demokradiyya wanda ake yi a ranar 12 ga watan Yunin kowace shekara.

Sanarwar ta fito daga bakin mai magana da yawun hukumar ‘ƴan sandan farin kaya ta DSS, Dakta Peter Afunanya inda ya ce hukumar ba zata amince da dukkan nau’in tada-zaune-tsaye gami da karya doka da odar ƙasa ba.

Peter ya ce, sun samu rahotanni dake batun cewa akwai mutane daban-daban da suka shirya gudanar da zanga-zanga a wurare da dama a ranar demokradiyya wanda ka iya barazana ga zaman lafiyar al’ummar ƙasa duk da cewa akwai damar bayyana ra’ayi a dokar ƙasa.

Ya ƙara da cewa ba za su amince da dukkan zanga-zangar da ka iya haifar da tarzoma ba, a madadin haka, ya ce ƴan ƙasa suna da ƴancin bayyana ra’ayi ta hanyar lumana.

Ɗaya daga cikin abun da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu zai yi jawabi a kai a ranar, shine batun mafi ƙarancin albashi ga ma’aikata wanda yana daga cikin batutuwan da suka dami al’ummar Najeriya.

Daga ƙarshe, sanarwar ta ce hukumar zata yi aiki da sauran ɓangarorin tsaro wajen tabbatar da tsaron ga dukiyoyi da rayukan al’umma inda ta ce ƴan kasuwa su fito kasuwancin su cikin lumana.

By Babaji