Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Domin murnar zagayowar ranar Dimokuradiyya a Nijeriya gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya bayar da umarnin a saki fursunoni 110 daga gidan gyaran hali da ke jihar.
Gwamna Sani ya yi haka ne somin tabi na wani a zaman wani bangare na bikin ranar dimokradiyya na bana da kuma murnar cika shekara guda a kan karagar mulki.
Gwamna Sani tare sa wasu manyan jami’an gwamnati sun ziyarci gidan gyaran hali na jihar Kaduna tare da fitattacen lauya Femi Falana (SAN), inda ya bayyana bukatar a yi garambawul a gidajen gyaran hali da ke jihar Kaduna.
Ya kara da cewa matakin da ya dauka na sakin fursunonin 110 ya je daidai da ikon da ya ke da shi a karkashin tanadin sashe na 212 na kundin tsarin mulkin Nijeriya na shekarar 1999.
A nasa bangaren, Falana ya yaba wa Gwamna Sani bisa afuwar da ya yi wa fursunonin.
Ya kuma yi kira ga manyan alkalan jihohi da su ba da umarnin a rinka gudanar da bincike lokaci zuwa lokaci a ofisoshin ‘yan sanda a jihohinsu don duba batun tsare mutane ba bisa ka’ida ba, ya kuma yi kira ga gwamnonin jihohin kasar da su ba da fifiko wajen gyaran cibiyoyin gyaran halin da ke jihohinsu.
An dai gina gidan gyaran hali na Kaduna a shekarar 1915 ne, wanda zai iya daukar fursunoni 500.
Amma a halin yanzu, cibiyar tana da fursunoni sama da 3,000 a cikin ta, yayin da wadanda ke jiran a yanke musu hukunci suke birjik a gidan ba tare da an waiwayesu.
