Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan ya yi zargin cewa wasu gwamnonin jihohi sun shagaltu da karfafawa masu aikata laifuka don amfani da su wajen cimma manufar siyasa, maimakon karfafa gwiwarsu su zama kwararru a ma’aikatun gwamnati.
Jonathan ya bayyana hakan ne a ranar Laraba a Benin yayin da yake kaddamar da sakatarorin jihar da Gwamna Godwin Obaseki ya gyara.
Tsohon shugaban kasar ya ce, lokacin da shugaban ma’aikatan ya bayyana cewa Obaseki ya dauki wadanda suka kammala digiri na farko aiki, ya ji dadi matuka, yana mai cewa “yana bukatar wani mai hangen nesa kamar Obaseki ya yi hakan”.
Ya ce, “A gaskiya idan ka je wasu jihohi, gwamnoni sun shagaltu da karfafawa masu laifi saboda siyasa, wadanda za su yi musu magudin zabe, dauke akwatunan zabe rike da wukake suna bin mutane a lokacin zabe.
“Amma daukar aikin kana karfafa masu kwakwalwa a jihar Edo. kwakwalwar ba ta fito daga jam’iyyar siyasa daya ba, ta fito ne daga dukkan jam’iyyun siyasa. kwakwalwar ta fito ne daga dukkan wadanda ke goyon bayan duk dan takarar gwamna.
“Wadanda suke yin digiri na farko su yi gwagwarmayar shiga samun sakamako na matakin farko maimakon shiga kungiyoyin asiri da shan barasa da yi wa mata fyade. Ya kamata ku yi kokari ku sami maki mai kyau. Don haka, idan kuna da damar zuwa makaranta, ku dauki makarantarku da mahimmanci.
Jonathan ya lura cewa, Obaseki baya goyon bayan wasu domin yana son ya ci zabe, sai dai don yana son gina jihar ne, inda ya kara da cewa: “ Ku gina jiha sai ku gina mutane.”
