
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
An samu rahoto daga Jihar Sakkwato dake cewa ƴan bindiga sun kai hari ƙauyen Dudun Doki a ƙaramar hukumar Gwadabawa da asuban ranar Lahadi.
Yayin da al’ummar musulmi ke bikin sallah, mutanen ƙauyen sun kasance cikin jimami da alhini ganin cewa ƴan bindiga suka kashe kimanin mutane goma tare da yin garkuwa da wasu da dama waɗanda kawo yanzu ba’a san adadinsu ba.
Jaridar Alfijir ta ruwaito cewa, ƴan bindigan sun kai harin ne da misalin ƙarfe 1:30 na dare.
