Da ƊUMI-ƊUMI: Gwamna Raɗɗa ya rubuta takardar tuhuma ga Sarkin Katsina

Spread the love

Gwamnan Katsina, Dikko Raɗɗa ya rubuta takardar tuhuma ga Sarkin Katsina Abdulmumini Kabir Usman.

Wannan al’amari ya jawo mutane da dama na tunanin kar abinda ya faru Jihar Kano da Sokoto ya maimaita kan shi a Jihar. Dalilin wannan tuhuma shine, rashin zuwa hawan Sallah da wasu masu anguwanni ba suyi ba sati biyu da ya wuce. Wannan a na ganinshi kamar rashin bin doka ne da kuma rashin ɗa’a ga martabar masarauta.

Duk da haka wasu suna tunanin dalilin yafi wannan. Gwamna Raɗɗa na tunnain ƙarfin masarautun yayi yawa.

Don haka dole ya rage masu ƙarfi ta hanyar yin wasu canje canje da ya kamata. Yin haka zai zama Gwamna zai ba wa yan adawar sarkin wasu muƙamai masu karfi a cikin fada.

By ukarofi