Daga USMAN NASIR KAROFI a Abuja
Alhaji Umar Ɗanladi Kilishi, ɗaya daga cikin ƙwararrun likitocin idanu daga arewacin Najeriya, ya rasu jiya Asabar a garin Kaiama da ke arewacin Jihar Kwara.
Marigayi Alhaji Kilishi yi aiki a asibitoci daban-daban a Kano, New Bussa da Ilorin.Sanarwar rasuwarsa ta fito ne daga bakin babban ɗansa, Mallam Ismaila Umar.
A lokutan da Arewacin Nijeriya ke fama da ƙarancin likitocin ido, Alhaji Umar Danladi Kilishi ya ziyarci asibitoci daban-daban a Nijeriya, domin yi wa masu ciwon ido aiki.
Marigayi likitan ido Kilishi, wanda a turance ana kiran su ‘Ophthalmologist’, ya rasu ya bar ‘ya’ya 10 da jikoki da dama. Mu na fatan Allah ya jiƙan sa, ya yi ma sa rahama.
