Me ya sa shahararrun mata ke wahalar auruwa?

Spread the love

Daga MUHAMMAD TAJAJJINI DAN TIJJANI

Abokina Sulaiman Badamasi ya yi tambaya a shafinsa na Fesbuk kamar haka: Me ya sa shahararrun mata ke wahalar auruwa?

Mata da yawa a nan Social Media masu tarin mabiya, masu son addini, kyawawa, su na posting abubuwa masu amfani.

Idan sun yi comment ko su ka sanya hoto, cikin ƙanƙanin lokaci za ka ga comments na yabo fiye da 1,000.

Me ya sa duk da wannan yabon da maza suke yi musu, suke daɗewa babu aure? Me ya sa ba a auran su?

Ga amsar da na ba shi:

Ingiza Mai Kantu Ruwa ake musu malam.

Mutane da yawa na sha’awar sheɗanci don nishaɗi da barƙwanci amma ba sa son a gansu suna yi don kar mutuncinsu kimarsu da martabarsu su zube a idon jama’a.

Amma in suka ga wani ko wata na yi sai abin ya dinga birgesu su dinga jin daɗi suna ba su goyon baya suna yi musu jinjina da kyauta ko su dinga Danna musu Like a soshal midiya. 

To, duk inda ka samu tantirin shaƙiyi mara kunya wanda bai san darajar kansa ba ko kare mutuncin gidansu da iyayensa ba sai ya fito ya kama sokonci ana tafa masa gani yake birgewa ne ya zama tauraro.

Inda gizo ke sakar shi ne in aka zo yin wani na karamci kamar ace yana son ya yi aure ko aka nemi aurenta za ka samu babu wanda yanke son ya gurɓata jininsa ko danginsa da ɗan iska ko fitsararre irin waɗannan.

Ire-irensu a fannin baɗala da saɓawa Allaah suke birgewa amma a fannin kamala da ayyukan alkhairi ba su da wani abin a zo a gani. Shi ya sa da yawa ba a son haɗa aure da su don lalata zuri’a da asali hakan ke haifarwa.

Ba ka ga Allaah SWT Yana cewa a Surah Nur Aya ta 2ɓ Munanan kalamai (ko Mata) na munanan mutane ne sannan munanan mutane na munanan kalamai (mata) ne ba. Hakazalika kyawawan kalamai (mata) na kyawawan mutane ne sannan kyawawan mutane na kyawawan kyawawan kalamai (mata) ne.

Kuma a wata ayar Ya ce mazinaci sai mazinaciya ko arne, sannan mazinaciya sai mazinaci ko arne. To mutumin da ake tir da halayyarsa yaushe za ka je ka haɗa dangi da shi ko da ita? Ai hauka ne yin hakan.

Ni dai a tunanina ka ji dalilin da ya sa ake ƙyamar auren ire-iren shahararrun mata musamman in shahararsu a fagen shagala da sharholiya ne. Su kuma mata masu kuɗi rashin girmama miji, yi masa biyayya da kuma gudun gori ne.

*Suleman Badamasi ne ya buƙaci na yaɗa wannan tambaya da amsar tamu ko jama’a za su ƙaru da rubutun namu. Za ku iya tofa albarkacin bakinku mu ji ra’ayinku. Muna godiya…

©2024 Tijjani M. M. marubuci ne, mazaunin Kano
A kiyayi haƙƙin mallaka

By ukarofi