Daga ALI ABUBAKAR SADIƘ
Idan ka zama sakarai, babu abinda ba za a yi ma ka ba. Sakamakon zama sakarkaru, saboda hassada da haɗama a arewacin Najeriya mu na ji muna gani an kassara mu ta ko’ina.
An cuso ma na Boko Haram ta mummunar akidar addini ta rashin hakuri da juna (tolerance) wadda ya kassara Arewa maso Gabas. Da aka ga aƙidar Boko Haram ba za ta karɓu a Arewa maso Yamma ba sai aka fara far ma Fulani a ko’ina suke, ana kashewa da ƙone mutanensu da dabbobinsu, wanda ya haifar mana da banditry da kama mutane domin kudin fansa.
Duk mai hankali ya san cewa akwai ajanda ta rusa Arewa daga ƙasashen Yamma, saboda babu abinda su ke yaki da shi irin yawan al’umma, kuma arewacin Najeriya ya zama yanki da ya fi ko’ina a faɗin duniya hayayyafa cikin gaggawa.
Manyan mu na banza, sun kasa game cewa maganin matsalar Arewa daya ce, wato rarraba arziki ta hanyar samar da ayyukan yi. Ga mu dai a Arewa Allah ya yi mana komai (yawan al’umma, ƙasar noma, albarkatun karkashin kasa, albarkatun ruwa), amma an wayi gari mun rasa komai (ba ilimi, ba aikin yi, ba kiwon lafiya sai bakin talauci da baki Hali).
Yanzu kuma an fito da sabuwar fitina ta kassara masarautunmu. Sarki biyu a Kano, an kassara karfin ikon Sarkin musulmi da kamo hanyar tube shi, an tozarta Gidan Ado Bayero da wulaƙanta tsatsonsa ta hanyar amfani da wata yarsa da ke Lagos wadda ta kasa biyan kudin haya. Yan siyasarmu manya su na kallo an jefa mutane cikin talauci sun kauda Ido, su na ta ƙulle-ƙulle ya za su karɓe mulki hannun Tinubu a 2027, saboda shine kawai abinda ya dame su.
Su waye su ka kai Tinubu Ɓilla? Ba irin kiran da ba mu yiwa su Atiku su hade kai su raba Najeriya da APC a 2023 ba, amma saboda bukatarsu kawai ita ce buƙata su na kallo Tinubu ya ci zabe da ƙuri’a miliyan takwas su kuma su na da kuri’a miliyan kusan 14 da su ka tsitstsinka. Wallahi a tarihin siyasar duniya ba ka taba ganin kidahumanci irin haka ba?
Sai a Najeriya saboda son kai, sai yanzu ne za su hada kai? Kuma duk masifar da Najeriya, musamman Arewa ke ciki wa janyo ta idan banda zaluncin mulkin Buhari na shekaru 8, amma sai ga shi su Atiku na ziyararsa ana ta wasu kulle kulle.
Wallahi Arewa na daf da rushewa kuma idan ta rushe ba wanda zai tsira a cikinmu, manya da kanana. Ko dai mu farka daga barci mu daina hassada da handama mu tashi tsaye wajen tirsasa gwamnoni su saka kudaden al’umma a ayyuka da zasu samar da ayyukan yi, a yaƙi talauci ko kuma ba wanda zai zauna lafiya.
An kassara tattalin Arewa maso gabas an kassara na Arewa maso yamma. Kano da Jigawa kaɗai ke zaune lafiya yanzu ana hura wutar da zata kassara Kano, wallahi ana kassara Kano shi ke nan mun gama rushewa kuma ana kan hanya. A 2019 na yi wani rubutu da na ja hankalin yan Arewa cewa an saka mu a gaba fa, kuma a lokacin Borno da Zamfara kaɗai ke cikin tashin hankali. Na ce mu lura sauran jiihohin Arewa zasu iya samun kansu a wannan yanayi idan muka cigaba da watsi da barazanar, amma kafin Buhari ya sauka, Kano da Jigawa kadai ke zaune lafiya.
Zan maimaita, matukar bamu farka ba, kafin 2027 sai an tarwatsa Kano. Mu na fuskantar mummunan hatsari amma an rasa wadanda za su ja kunnen Kwankwaso da Ganduje, Sunusi da Aminu, to idan Kano ta lalace na ga uwar da zasu mulka. Allah ka iya ma na ba don iyawarmu ba, ka yi mana sakayya a kan wadannan yan siyasa da masu mulki da ba sa son mu, sai don biyan bukatarsu, domin martabar Musa da Isa, don Martabar Ibrahimu da Mahammadur Rasulillah.
Sadiƙ mai sharhi kan al’amuran yau da kullum ne a Kano
