Harin Gwoza: Red Cross za ta taimaka wa asibitin Maiduguri

Spread the love

Daga EDITA

Tawagar Likitoci daga ƙungiyar agaji ta ‘International Committee of the Red Cross’ (ICRC), za ta tallafa wa likitocin asibitin Maidugiri wajen yi wa mutanen da harin ƙunar baƙin wake a Gwoza ya afka mu su magani.

Cikin wata sanarwa da ƙungiyar ta fitar, ta ce tawagar ƙwararrun likitocin nata za ta yi aiki da likitocin asibitin koyarwa na birnin Maiduguri wajen ceto rayukan mutanen da harin ya yi musu mummunar illa.

Mutane da dama ne suka samu munanan raunuka a lokacin harin da wasu ƴan ƙunar baƙin wake suka kai garin Gwoza a ƙarshen makon da ya gabata.

An kai mutum 41 da suka jikkata zuwa asibitin na Maiduguri, da suka haɗa da mata da ƙananan yara a ranakun Asabar da Lahadi domin ba su kulawar gaggawa.

‘BBC Hausa’ ta ruwaito cewa ƙungiyar ICRC, ta bayar da tallafin magunguna da wasu kayayyaki ga asibitin domin taimaka wa ɓangaren kula da masu buƙatar kulawar gaggawa.

Mataimakiyar shugaban tawagar ƙungiyar da suka je Maiduguri, Diana Japaridze ta ce halin da marasa lafiyar ke ciki a asibitin ”abin tayar da hankali ne”.

“Muna kira da babbar murya cewa, a yaƙi, dole ne a kare fararen hula musamman mata da ƙananan yara, kuma asibiti wuri ne na ceton rai, ba wurin salwantar da rai ba.”

A ranar Asabar ne wasu mata huɗu suka tayar da boma-bomai a wurare daban-daban a Gwoza lokacin da ake tsaka da bikin aure, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutum 32 tare da jikkata gommai, kamar yadda mataimakin shugaban ƙasar ya bayyana, inji BBC Hausa.

By Babaji