Kwamishinonin El-Rufai sun zargi Gwamna Sani da ƙoƙarin zubar ma sa da ƙima

Spread the love

Tsohon Gwamnan Kaduna, Mal Nasiru Elrufa’i ya zargi Gwamna mai ci, Uba sani da ƙirƙirar ƙudin da babu, cewa an karkata su. Yace wannan bita da ƙulli ne kawai na siyasa.

A wani taron manema labarai da tsofaffin Kwamishinonin Elrufa’i sun musanta zargin da ake ma Elrufa’i, sunce wannan kawai an faɗa ne amma babu gaskiya a cikin lamarin. Ana yin haka ne kawai domin cin mutunci.

Kwamisshinonin wanda sukai aiki lokacin Elrufa’i sunce kuɗin da ake cewa an karkata babu su, sabida idan ka duba rahoton nasu, basu faɗi yadda suka samo su ba.

Sun ƙara da cewa, idan akai duba na tsanaki, za a ga yadda wasu abubuwa dayawa a cikin rahoton da basu bada ma’ana ba.

By ukarofi