Ɗan sanda ya mutu a harin da aka kai wa Shaibu kwana ɗaya bayan kotu ta maida shi kujerar Mataimakin Gwamnan Edo

Spread the love

Wani jami’in ‘yan sanda mai suna Okon, wanda ke da tare da ɗan takarar jam’iyyar APC a zaɓen gwamnan Jihar Edo da aka yi a ranar 21 ga watan Satumba, ya rasa ransa bayan wasu ‘yan bindiga sun kai hari kan ayarin motocin shugaban sa da na Mataimakin Gwamnan jihar, Philip Shaibu, a Benin.

Shaibu, wanda majalisar dokokin jihar ta tsige shi a ranar 8 ga watan Afrilu, amma kotu ta dawo da shi, bayan mai shari’a J.K. Omotosho ya ce an tsige shi bisa rashin adalci.

Shaibu da Okpebholo sun isa filin jirgin sama na Benin da misalin karfe biyu na rana don tarbar magoya bayansu.

Ma’aikatan filin jirgin sun bayyana cewa, yadda jami’an ‘yan sanda suka yi a kusa da Shaibu alama ce da ke nuni wani abu mara kyau zai faru.

Lokacin da ayarin motocin suka bar filin jirgin, wasu ‘yan bindiga ɗauke da makamai sun harbi ayarin motocin, lamarin da ya kai ga mutuwar ɗan sandan.”

Wani shedar gani da ido mai suna John ya ce baya ga ɗan sandan, wasu sun jikkata a harin.

Ya ce, “Lamarin ya faru ne bayan karfe 2 na rana. lokacin da Okpebholo da wasu da dama, ciki har da mataimakin gwamnan jihar, Philip Shaibu, suka isa cikin wani jirgi mai zaman kansa na haya.

Ya ce, “Lokacin da jirgin ya sauka, yadda jami’an ‘yan sandan suka yi a kusa da Shaibu ya nuna cewa wani mugun abu na shirin faruwa.

By ukarofi