Mai horas da Tawagar Ƙwallon Ƙafa ta Mata ta Nijeriya Randy Waldrum, ya ce tawagar ta shirya don tunkarar gasar Olympics da birnin Paris zai kar baƙunci, duk kuwa ta makarar zuwa sansani da wasu ’yan wasa suka yi.
A wata zantawa da aka yi da shi, Waldrum ya ce duk da rashin isowar wasu daga cikin ’yan wasan tawagar akan lokaci, amma sun yi ƙoƙarin sajewa da sauran da suka iso da wuri.
Wannan ne dai karo na farko a cikin shekaru 16 da tawagar ta samu gurbin buga gasar Olympics, inda ta kasance daya daga cikin tawagogin ƙasashen Afrika da za su wakilci nahiyar a gasar.
Tawagar ta Super Falcons za ta isa birnin Bordeaux na Faransa, don shirya wa wasansu da Brazil a ranar Alhamis mai zuwa, sannan ta kuma karawa da Spain a ranar 28 sai kuma Japan a ranar 31 ga wannan wata na Yuli da muke ciki.
Tawagar ta Super Falcons da ta kai matakin zagayen daf da na kusa dana ƙarshe a gasar ta shekarar 2004, ana ganin ta faɗa cikin rukuni mafi zafi a wannan gasa.
A gasar Olympics da aka gudanar a Atlanta a shekarar 1996 ne aka fara wasan ƙwallon kafa ta mata a wannan gasa, inda tawagar ta Super Falcons kuwa ta fara halartar gasar ne a shekarar 2000, kuma ta yi rashin nasara a hannun China da ci 3-1 sai kuma ta samu nasara a kan ƙasashen Norway da Amurka.
Rahotanni na cewa an bayyana lambobin rigunan ’yan wasan tawagar ƙwallon ƙafar mata ta Nujeriya, wato Super Falcons, waɗanda za su fafata a ɓangaren ƙwallon ƙafa a gasar wasannin motsa jiki ta Olympics.
Falcon za su koma wannan gasa ce bayan da aka shafe shekaru 16 ana yi ba tare da ita ba.
Mai tsaron ragar Nijeriya, Chiamaka Nnadozie ce aka bai wa riga mai lamba 16, ita ko ’yar wasan gaba, Asisat Oshoala za ta ci gaba da sanya riga mai lamba 8, a yayin da ’yar wasan tsakiya ta Benfica, Christy Ucheibe za ta saka riga mai lamba 10.
Kyaftin na tawagar, Rashidat Ajibade aka bai wa riga mai lamba 15, a yayin da mai tsaron baya, Osinachi Ohale ta ci gaba da riƙe rigarta mai lamba 3.
Tawagar Super Falcons za ta fafata da takwararta ta ƙasar Brazil a wasanta ta farko a ranar Alhamis, 25 ga watan Yuli a filin wasa na Stade Bordeauɗ.
Sauran wasannin matakin rukuni da Nijeriya za ta fafata za su kasance ne tsakaninta da Sifaniya a ranar 28 ga watan Yuli, sai karawarta da Japan a ranar 31 ga watan Yuli, wasanni da za a yi a filin wasa na Stade de la Beaujoire a birnin Nantes.
