Yadda zanga-zangar matsin rayuwa ta ƙazance a Nijeriya

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Zanga-zangar nuna adawa da tsananin matsin rayuwa da ake ciki a Nijeriya wadda aka fara gudanarwa jiya Alhamis a duk faɗin ƙasar ta bar baya da ƙura a wasu jihohi, inda ake zargin wasu ɓata-gari da yin amfani da zanga-zangar wajen ɓata kayan gwamnati da fasa shagunan ‘yan kasuwa ana sace kayan masarufi da wasu muhimman abubuwa da sauran ayyukan dabanci, lamarin da ya jefa al’umma cikin zulumi da takaici.

Babban abin da matasan ke dogaro da shi game da kiraye-kirayen su na yin zanga-zangar shi ne matsin tattalin arziki.

Al’ummar ƙasar na kokawa kan yadda tashin farashin kayan masarufi ya sanya suke gaza sayen abubuwan buƙatu na rayuwa, yayin da ake zargin cewa talauci ya yi yawa ta yadda wasu mutanen ba su da tabbacin samun cin abinci ko da sau ɗaya a rana.

nie ɗauka.

Hauhawar ta fi shafar kayan abinci inda sabbin alƙalumman na hukuma suka ce ya kai kashi 40.87 a watan Yunin 2024 idan aka kwatanta da Yunin 2023 inda aka samu ƙaruwar kaso 15.6.

Tun bayan da gwamnatin Najeriya ƙarƙashin shugaba Tinubu ta cire tallafin man fetur a ranar 29 ga watan Mayun 2023, farashin kayan masarufi ya ci gaba da ɗagawa.

Da farko dai farashin litar man fetur ya nunka kusan sau huɗu, lamarin da ya sanya farashin sufuri ya tashi, haka nan ma na kayan abinci da sauran kayan buƙatu, lamarin da ya ingiza matasa fara gudanar da zanga-zangar lumana duk da kiraye-kirayen da shugabanni da malaman addini suka dinga yi akan illolin yin zanga-zangar.

MANHAJA ta haƙaito yadda zanga-zangar ta kasance a wasu jihohi kamar haka:-

Ɓata-gari sun sauya zanga-zanga a Kano, sun koma sata da lalata muhimman wurare:

Zanga-zangar da aka yi a Kano ta rikiɗe zuwa tashin hankali, yayin da wasu ɓata-gari suka karɓe zanga-zangar inda suka farfasa shaguna da ofisoshi.

Manhaja ta rawaito cewa ɓata-garin sun fara kai hare-hare kan shaguna da ofisoshi inda suke gudanar da ayyukan dabanci iri-iri a kan tituna.

An ga yadda a wasu wawure ɓata-garin ke wawason dukiyar jama’a da kayayyaki masu daraja da suka haɗa da kujeru, kwamfutoci da sauran kayayyaki masu tsada.

An kashe mutum ɗaya yayin wawaso a rumbun abincin gidan mahaifiyar Ɗangote:

Rahotonni daga jihar Kano na cewa an kashe mutum ɗaya yayin da wasu ɓata-gari suka fasa wurin ajiyar kayan abinci mallakar Hajiya Mariya Sanusi mahaifiyar Aliko Ɗangote.

Wani da ya shaida lamarin ya bayyana cewa masu wawason sun kwashe kayan abinci da dama kafin ‘yan sanda su ƙarasa wurin, inda suka kwashe sauran abin da ya rage.

“Yanzun nan muka dawo daga maƙabarta, sun kashe ɗan yayarmu a wurin,” kamar yadda wani da ya shaida yadda abin ya faru ya faɗa wa BBC.

Lamarin ya faru ne a unguwar Ƙoƙi da ke cikin ƙaramar hukumar Birni, wurin da Mariya Sanusi ke da wuraren ajiyar kayan abinci da ake girkawa domin tallafa wa marasa ƙarfi a faɗin jihar ta Kano.

Gwamnatin jihar ta sanya dokar hana fita tsawon awa 24:

Gwamna Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya ayyana saka dokar hana fita tsawon awa 24 a birnin jihar.

Ya bayyana haka ne a jiya lokacin da yake wa manema labarai ƙarin bayani.

Gwamna ya bayanna cewa ɗaukar wannan doka na da nasaba da yunƙurin da ake yi na ci gaba da tashe-tashen hankula dake gudana da sunan zanga-zangar lumana da ake gudanarwa a faɗin ƙasar nan baki ɗaya.

Gwamnan ya kuma buƙaci jami’an tsaro da su ƙara ƙwazo wajen aiwatar da aikin su don kare al’umma da dukiyoyinsu.

An kashe masu zanga-zanga shida a Jihar Neja:

Aƙalla mutane shida ne aka ruwaito sun mutu yayin da wasu suka samu raunuka a zanga-zangar da ake ci gaba da yi a garin Suleja na jihar Neja.

An ce waɗanda harin ya rutsa da su an kashe su ne a yayin da jami’an tsaro ke ƙoƙarin tarwatsa gungun masu zanga-zangar da suka yi shinge a wani ɓangare na babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Wannan jarida ta ba da rahoton yadda fasinjoji da masu ababen hawa suka maƙale a hanya tsawon sa’o’i.

Wasu ’yan sandan da ke kewaye da shingayen sun kasa shawo kan matasan da suka fi su yawa.

Koyaya, an aika da ƙungiyar ƙarfafawa zuwa wurin da bala’in ya faru.

Daga cikin waɗanda aka kashe har da Yahaya Nda Isah, mazaunin titin Hassan Dalatu, Suleja, wanda harsashi ya same shi.

An bayyana cewa harsashin ya afkawa Isa ne akan babur ɗin sa a gaban sashin ‘yan sanda na Suleja inda masu zanga-zangar suka taru.

Wani ɗan uwa ga marigayin ya shaida wa wannan jarida cewa kawun nasa yana kan babur ɗinsa ne harsashin da aka harba don tarwatsa masu zanga-zangar ya same shi a ƙirjinsa kuma nan take ya mutu.

“Shi ne kawuna. Bai ko yi zanga-zanga ba. Yana wucewa ne a gaban sashen ‘yan sanda ‘A’ inda wasu mutane ke zanga-zangar sai harsashin da ya fita ya same shi a ƙirjinsa ya mutu. Yayin da nake magana da ku, ina cikin gidansa tare da sauran masu makoki. Abin takaici ne,” in ji shi.

Wani da aka kashe mai suna Malam Abu shi ma ya ce a nan take ya mutu.

Ɗaya daga cikin mazauna yankin da bai so a ambaci sunansa, ya shaida wa wannan jarida cewa an harbe wasu mutane 3 a wuri guda yayin da wasu 2 kuma aka harbe su a mahaɗar Suleja da ke kan hanyar Abuja zuwa Kaduna amma bai iya tabbatar da ko wasu da abin ya shafa sun mutu ba.

Wani mazaunin garin da ya ce shagon nasa ba shi da nisa da sashin ‘yan sanda na Suleja “A” ya ce sai da ya rufe domin ya tsira da ransa.

“Mun ji mutane suna ihu, an kuma ji ƙarar harbe-harbe na kusan mintuna 20 a sha-tale-tale na Sarki. Halin da ake ciki a Suleja ya yi muni,” Bala Abdullahi, wani mazaunin garin.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Neja, SP Wasiu Abiodun, ya ce wasu ‘yan daba sun kuma yi yunƙurin banka wa Sakatariyar Ƙaramar Hukuma a Tafa wuta amma jami’an tsaro suka tarwatsa su.

“’Ɓata-gari sun yi yunƙurin bankawa Sakatariyar Ƙaramar Hukuma a Tafa wuta, ‘yan sanda da sojoji sun tarwatsa su. An share hanyar Kaduna da kuma shingen,” inji shi.

Da aka tuntuɓi jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sanda a Neja, Wasiu Abiodun ta wayar tarho, ya ce, “Bari in tantance in dawo gareku.”

Kiristoci sun ba Musulmi kariya wajen zanga-zanga yayin da suke sallah a Jos:

A wani abin farin ciki da ya faru yayin zanga-zanga a Jos, shine Kiristoci sun ba Musulmai kariya yayin da suke sallar Azahar a filin zanga-zanga.

Wannan na zuwa ne a lokacin da rikicin addini ya yi ƙamari a jihar amma da irin wannan haɗin kan, za a iya cewa lallai matasa sun fara gane abinda ke masu ciwo kuma za su kawo ci gaba nan gaba mai ɗorewa.

Wani shaidar gani da ido ya bayyana cewa, wannan abun da ya faru ya nuna cewa, Kiristoci da Musulmai kan su haɗe yake, wasu ɓatagari ne ko a can baya ke son raba wannan haɗin kan.

Kuma wannan wata alama ce da ke nuni da cewa, in dai muka haɗa kawunanmu to za mu samu ci gaba fiye da yadda muke tunani. Kuma wannan hotunan da ke yawo za su ƙara na saura sassan ƙasar nan ƙwarin gwiwa yadda ya dace.

Jami’an tsaro sun mamaye titinan Abuja:

Domin daƙile taɓarɓarewar doka da oda daga ‘yan Nijeriya masu zanga-zangar adawa da yunwa da matsin tattalin arziki, jami’an soji da ‘yan sanda sun mamaye sassa daban-daban na Abuja.

Wakilin jaridar Blueprint da ya ziyarci sassa daban-daban na babban birnin tarayya Abuja, ya lura da cewa an jibge jami’an tsaro da suka shirya yaƙar ɓatagari a wasu muhimman wurare na birnin.

Daga ƙaramar hukumar Bwari, an ga jami’an soji da ‘yan sanda waɗanda ke ɗauke da makamai, a rukunin Tipper Garage Junction, Signboard, Sokale, Kasuwar Dutsen Alhaji, Gadar Dutse Junction, Citec, Dawaki, Galadima da Mahaɗar Gwarinpa.

Wani abin sha’awa shi ne, titunan da ke da yawan jama’a ba su da zirga-zirgar ababen hawa saboda yawancin mazauna birnin sun gwammace su zauna a cikin gida, saboda tsoron abin da ka kai ya komo.

Haka kuma an jibge jami’an tsaro a mahaɗar Jahi, Katampe, Ministers Hill, Nicon junction, Banneɗ da Berger.

Da take magana da Blueprint, wata matafiya, wacce ta bayyana kanta a matsayin Blessing, ta ce tun yanzu tana fargabar shiga cikin masu zanga-zangar a kan hanyarta ta zuwa aiki, amma kasancewar jami’an tsaro da ke barazana ga lafiyarta ta samu kwanciyar hankali.

“Ba na son zuwa aiki a yau, amma babu wani uzuri na rasa aiki, don haka dole ne in je a kowane hali. Da tashe-tashen hankulan da aka samu a kafafen yaɗa labarai, na yi mamakin yadda ban ga wani ya yi zanga-zanga a ko’ina ba daga Bwari da nake zaune zuwa Gwarinpa inda nake aiki.

“A gaskiya, na ji daɗin yadda jami’an tsaro suka mamaye sassan titin. Daga ganin fuskokinsu, za su kashe duk wata matsala tun kafin ta faru. Duk da cewa na ji takaicin yadda mutane da yawa suka kaucewa zuwa yau domin har yanzu kasuwar Dutsen Alhaji ta kulle har ƙarfe 8:10 na safe, mutane kaɗan ne ke jira a bakin gate.

“Har ila yau, akwai ’yan direbobi a kan hanya, wanda zai sa sufuri ya yi wahala ga waɗanda ba su da motoci. Amma duk da haka ina so in ba duk wanda ke son fitowa ya yi hakan domin sojoji da jami’an ‘yan sanda ba sa cin mutuncin kowa ku fito ku yi duk abin da kuke so cikin kwanciyar hankali ba wanda zai dame ku.”

Shi ma da yake zantawa da wakilinmu, wani direban tasi mai suna Adebayo, ya ce titin ya bushe ba kamar yadda ya saba ba, kuma ya tilasta masa ya ƙara kuɗin tafiya saboda rashin fasinja da kuma inda zai sayi mai.

“Idan ban ga fasinjoji kafin rana ba, zan koma gida saboda ba zan iya yin asarar mai na ba. Hanyoyin sun bushe, don haka na ƙara Naira 200 ga waɗanda za su je Berger saboda ba zan iya ɗaukar mutum ɗaya ko biyu a wurin a kan farashi na yau da kullum ba. Ban san dalilin da ya sa mutane ke magana game da zanga-zangar ba, ba zai canza komai ba. ‘Yan sanda za su harbe ka kawai kuma hakan ne zai ƙare,” inji shi.

Kamfanin Dillancin Labaran iƙna ya habarta cewa, ya nakalto daga shafin sadarwa na yanar gizo na Blueprint cewa, an rufe gidajen mai da bankuna da sauran cibiyoyin da suka fito daga Bwari zuwa Gwarinpa ga jama’a saboda jami’an tsaro ne kawai aka hango a tsaye a gaban kofofi daban-daban.

Idan ba a manta ba, wata babbar kotun birnin tarayya, Laraba, ta umarci masu zanga-zangar da su taƙaita ayyukansu a filin wasa na Moshood Abiola kawai.

Kotun ta yanke hukuncin ne saboda damuwa game da yiwuwar kawo cikas ga zaman lafiya da amincin jama’a daga masu zanga-zangar.

Sufeto Janar na ‘yan sandan dai ya umurci jami’an tsaro da su ba da cikakkiyar kariya a cikin filin wasan yayin zanga-zangar.

An sanya dokar hana fita a ƙananan hukumomi uku na Yobe:

Gwamnatin Yobe ta sanar da sanya dokar hana fita ta sa’o’i 24 a ƙananan hukumomi uku na jihar.

Ƙananan hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da Potiskum, Nguru, da kuma Gashua.

Hakan dai na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da mashawarcin gwamnan jihar na musamman kan harkokin tsaron, Birgediya-Janar Dahiru Abdulsalam mai ritaya ya fitar a jiya Alhamis.

Sanarwar ta ce ɗaukar matakin ya zama tilas la’akari da yadda wasu ɓata-gari ke fakewa da zanga-zangar matsin rayuwa suna sacewa da lalata kadarorin jama’a da na gwamnati.

Abdulsalam ya ce a yayin da ake umartar jami’an tsaro da su tabbatar an kiyaye dokar, yana kuma shawartar jama’ar ƙananan hukumomin da su zauna a gida domin tabbatar da zaman lafiya da tsaro.

Kazalika, Gwamna Mai Mala Buni ya yaba wa al’ummar jihar musamman matasan da suka amsa kiran janyewa daga zanga-zangar matsin rayuwa la’akari da ƙalubalen tsaro da ake fuskanta a jihar.

An kama masu zanga-zanga 24 a Kaduna:

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kaduna ta ce ta kama mutum 23 cikin masu zanga-zangar nuna fushi kan matsin rayuwa a jihar.

Mai magana da yawun rundunar, Mansur Hassan ya tabbatar wa Manhaja cewa waɗanda aka kaman sun yi ƙoƙarin kutsawa ne zuwa cikin gidan gwamnati.

Ya kuma ce mutanen sun yi ɓarna kala-kala a lokacin zanga-zangar.

“Sun ƙona motarmu ta APC, sun ƙona babban ofishin Kastelia sun farfasa ofishin Kadipa sun kwashe kaya.”

Ya bayyana cewa dama sun samu bayanai na tsaro da suka nuna cewa waɗanda ke yin zanga-zangar za su fake da ita domin aikata laifi.

Sai dai jami’in ya musanta cewa an kashe mutum ɗaya a cikin masu zanga-zangar.

An kashe mutum huɗu a Borno, uku a Jigawa da dama a Katsina:

An ce mutane da dama sun mutu bayan da ɓata-gari suka shiga zanga-zangar, inda suka yi awon gaba da kaya a shaguna daban-daban tare da lalata dukiyoyin mazauna garin.

Hakan ya faru ne kafin masu zanga-zangar su isa inda suka shirya gudanar da muzaharar.

An tilastawa wasu jami’an tsaro harbi kan matasan da suka gudanar da zanga-zangar domin tabbatar da doka da oda wanda hakan kuma ya tarwatsa masu zanga-zangar.

News Point Nigeria ta samu labarin cewa wasu daga cikin waɗanda lamarin ya rutsa da su da suka haɗa da jami’an ‘yan sanda da DPO, an yi musu jinya iri-iri a wani asibitin fadar gwamnatin jihar Katsina.

Sai dai ƙoƙarin yin magana da kakakin rundunar ‘yan sandan Abubakar Sadiƙ ya ci tura domin ba a samu lambar wayarsa ba.

Rahotanni sun yi nuni da an kashe masu zanga-zanga huɗu a tashar Kime, Bolori Junction a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, ranar Alhamis.

Jami’an gidan mai da suka bayyana mamacin a matsayin ma’aikacinsi, sun bayyana yadda suka mutu daban-daban.

“Kamar yadda nake magana da ku, har yanzu suna kwance a cikin jini,” in ji ɗaya daga cikin ma’aikatan da ya bayyana sunansa da Malam Musa.

Musa wanda ya tabbatar da cewa yana tare da waɗanda abin ya shafa ya ce sun mutu ne sakamakon fashewar wani abu.

“Ya kusa shafata, amma kamar yadda Allah Ya so, na tsira ba tare da jin rauni ba.”

Sai dai wata majiya mai tushe da ta nemi a sakaya sunanta ta ce harsashin da suka kai ga mamacin ya same su.

“Ni ina daura da gidan mai ne lokacin da lamarin ya faru, babu wani abu kamar fashewar bam, kawai mun ji ƙarar harbe-harbe kuma yaran sun faɗi. Hudu daga cikinsu sun mutu nan take,” inji shi.

Aƙalla mutane uku ne suka mutu sannan wasu da dama suka jikkata yayin da ‘yan sanda suka harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa ɓata-garin da suka kutsa cikin masu zanga-zangar #BadBadGoɓernance a ranar Alhamis a faɗin jihar Jigawa.

Jihar Jigawa ta fuskanci wani yanayi da ba a taɓa ganin irinsa ba a tarihin jihar yayin da zanga-zangar adawa da ƙunci da yunwa ta kunno kai a wasu manyan garuruwa sama da 10 a faɗin jihar tare da samun rahotannin ɓarna tare da wawashe dukiyoyin gwamnati da wasu baranda suka yi.

Rahotanni daga birnin Haɗeja sun tabbatar da mutuwar mutane biyu tare da kwantar da mutane huɗu a wani asibiti sakamakon raunuka da shakar hayaƙi da jami’an ‘yan sandan yaƙi da tarzoma suka harba musu, yayin da aka wawashe rumbun kayan abinci mallakar gwamnati a yankin.

An yi dafifi a gidan Buhari da ke Daura:

Wasu cincirindon matasa sun yi wa gidan tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari, a Daura da ke Jihar Katsina a yayin da zanga-zangar ƙalubalantar matsin rayuwa ta ɓarke a Nijeriya jiya, Alhamis.

Wani hoton bidiyo da Blueprint Manhaja ta gani ya nuna yadda matasan su ke iface-iface a ƙofar gidan, su na masu nuna takaicinsu da halin da su ke ciki tare da faɗin baƙaƙen maganganu akan tsohon shugaban ƙasar, inda suke nuni da cewa, shine ummul’aba’isin halin da suke ciki. Bugu da ƙari, an ga matasan su na ƙona tayoyi, don cigaba da nuna fushin nasu

By ukarofi