Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Dakarun rundunar sojin Nijeriya tare da hadin gwiwar ‘yan banga sun kashe ‘yan bindiga sama da 100 a kauyen Kundu dake karamar hukumar Wushishi a jihar Neja.
Dakarun sun yi arangama da maharan ranar Laraba da safe.
Jami’an tsaron sun samu wannan nasara bayan sun yi wa maharan zobe yayin da za su tsallaka zuwa Kontagora ta hanyar Akere dake Kundu.
Wani majiya daga Kundu ya bayyana wa Daily Post cewa sun samu labarin zuwa maharan akan baburan amma sai daga baya sun samu labarin maharan sun ajiye baburan su suna takowa a kasa.
Ya ce maharan sun yi haka ne bayan sun samu labarin tarkon da jami’an tsaron suka yi musu.
Ishaku Musa Kato mazaunin Wushishi ya ce sun ji karar harbin bindiga yayin da ake ruwan sama.
“Mun yaba kokarin da sojojin suka yi inda a wannan karon sun yi nasara akan maharan.
Kwamishinan tsaro na jihar Abdullahi Bello Mohammed shima ya yaba kokarin da jami’an tsaron suka yi sannan ya ce ba su da masaniya yawan maharan da suka ji rauni ko suka mutu.
“Idan abu ya faru irin haka maharan basa barin gawa ko wani nasu da ya ji rauni, tattara su suke yi su arce da su domin kasa ma a gani wani ko kuma wanda ya rayu ya fallasa su.
