Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano
Gwamnatin Jihar Yobe ƙarƙashin jagorancin Mai Mala Buni ta zo da kyakkyawan tsari na kyautata makomar yara da ake samu suna yawace-yawace akan manyan hanyoyi a jihar ta gina su akan neman ilimi da bunƙasa rayuwarsu.
Wannan nasara an same tane bisa irin ƙwazo da himma na Babban sakataren Hukumar kula da ilimin Arabiyya da harkokin addini ta jihar Yobe (AISEB), Malam Umar Abubakar.
Babban sakataren da ya samu kyakkyawar shaida na cewa tun naɗa shi daga tun 9 -10-2023 ya gudanar da ayyukan ci gaba da dama da a yanzu ake alfahari da su a jihar Yobe.
Hukumar ta samar da na’ura mai ƙwaƙwalwa ga alƙalai na musabaƙar Alƙur’ani domin inganta harkokin musabaƙa a jihar, ta samar da na’ura mai ƙwaƙwalwa a dukkan sashin dake hukumar da samar da kayan aiki domin inganta ayyyuka da take gudanarwa.
Babban sakataren na hukumar kula da ilimin Arabiyya da addini na Jihar Yobe Malam Umar Abubakar ƙarƙashin jagorancinsa ya samar wa almajirai yanayi mai kyau da kayan makaranta da kyautata wajen kwanciyarsu da sama musu allanu na karatu, tare da biya wa ɗalibai 50 kuɗin jarrabawar shiga makarantun gaba da sakandire.
Hukumar tasa ta yi ƙoƙari wajen ɗaukar nauyin ɗalibai ‘yan asalin jihar Yobe guda 32 domin yin karatu a Jami’ar Al-azhar ta Ƙasar Misira. Sannan ta yi jagoranci don gina makarantar sakandire mai suna makarantar sakandiren Al-azhar.
“Al-azhar Secondary School” a jihar Yobe domin magance matsalar tarnakin da ɗaliban jihar ke fuskanta yayin neman guraben karatu a ƙasar Misira.”
Cikin irin ayyuka da hukumar take ƙarƙashin jagorancin Malam Umar Abubakar akwai inganta rayuwar mata masu ƙaracin wadata ana ta zaƙulosu a ba su kayan sana’o’i da suka haɗa da kekunan ɗinki da baiwa matasa kayan sana’ar aski na zamani.
Hukumar ta kula da da ilimin Arabiyya da harkokin addinin ta Jihar Yobe ta yi rawar gani sosai wajen kula da bunƙasa cigaban rayuwar almajirai da karatun Alƙur’ani mai tsarki da duk a jihohin Arewa babu kamarta.Tana shirya masabaƙar Ƙur’ni na matakin jihar da shirya na waɗanda za su wakilci jihar a matakin ƙasa da duniya baki ɗaya.
Wannan irin ƙoƙari da kishi da jajircewa ta sa babban sakataren hukumar Malam Umar Abubakar ya samu lambar yabo da karramawa daga wurare daban-daban da suka haɗa da na “Khadimul Ƙur’an”, “Khadimul Ummah, Garkuwan Tsangayoyi da Islamiyoyi na Jihar Yobe,” har ma ake masa laƙabi da ‘Baban Almajirai’.
