Gwamnan Kano ya ɗora laifin caɓewar zanga-zanga kan magoya bayan Aminu Ado Bayero da APC

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano, ya ce tashin-tashina da aka samu a zanga-zangar tsadar rayuwa a jihar, aiki ne na wasu ɓata-gari da ke biyayya ga saukakken Sarki, Aminu Ado Bayero da kuma ƴan daba da jam’iyyar APC ta ɗauki nauyinsu.

Wasu matasa ɗauke da makamai sun kutsa Fadar gwamnatin jihar inda su ka yi ta ƙone-ƙone a farfajiyarta.

Abba ya ce, dubban ƴan zanga-zangar lumana ne su ka taru a wajen Fadar don su miƙa saƙon kokensu, inda daga baya ta sauya zani zuwa tarzoma.

Gwamnan ya ce, a lokacin da jami’ai su ka tarbi ƴan zanga-zangar a Fadar gwamnatin, kwatsam sai su ka ga waɗansu ƴan daba ɗauke da makamai daga gidan Nasarawa sun nufo inda aka taru.

Ya ce, “mun gode wa Allah, kun ga abin da ya faru jiya wanda hakan ya saɓa wa abin da waɗanda su ka shirya zanga-zangar su ka yi alƙawari na cewa za su yi ta cikin lumana, kuma dubban su sun fito inda su ka taru a Gidan Murtala”, inji shi.

Ya ƙara da cewa, jami’an tsaro sun ɗauki aƙalla sa’o’i uku su na watsa mu su hayaƙi mai sanya hawaye da aka fi sani da barkonon tsohuwa. A sanadiyyar haka ne su ka ja da baya sai su ka fara sata a gidaje, shaguna da wasu ofisoshin gwamnati gami da ƙona duk abin da su ka ci karo da shi ciki har da ofishin harkar na’urar komfuta da ake gaf da ƙaddamar da buɗe shi.

By Babaji