Mutane da dama sun raunata yayin da ƴan sanda suka tarwatsa masu zanga-zanga a Abuja

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

An samu mutane da dama da su ka samu raunuka a lokacin da jami’an ƴan sanda su ka tarwatsa taron ƴan zanga-zanga a birnin tarayya Abuja a ranar Juma’a.

Hakan na zuwa ne sakamakon watsi da gargaɗin da rundunar ƴan sandan ta yi mu su na hana su gangami da sunan zagayen tsadar rayuwa da ake ciki a birnin Abuja koma bayan inda kotu ta keɓanci mu su.

.

Wani shaida ya ce, ƴan sanda sun tarfa masu zanga-zangar ne jim kaɗan bayan sun wuce ta yankin asibitin Ƙasa inda jami’an su ka yi amfani da barkono tsohuwa wajen tarwatsa taron.

Wasu da su ka samu raunukan sun yi hira da ƴan jarida inda su ka yi alla-wadai da abin da ƴan sandan su ka yi mu su.

Haka kuma, an samu cecekuce a shafukan sada zumunta inda al’umma su ka yi ta tofa albarkacin bakinsu game da al’amarin.

Kawo yanzu dai ba a ƙididdige adadin waɗanda abin ya shafa ba. Sannan wasu masu kishi sun buƙaci a gudanar da bincike kan al’amarin tare da hukunta waɗanda ke da hannu acikin aukuwarsa.

By Babaji