Zanga-zanga: An sanya dokar hana fita a Jigawa

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi ya saka dokar hana fita na tsawon sa’o’i 24 a faɗin jihar sakamakon tashin-tashina da aka samu a rana ta farko na zanga-zangar tsadar rayuwa a Nijeriya.

Gwamnan ya ce, ba a so faruwar hakan ba inda daga baya aka ɗage dokar don al’umma su gabatar da sallar juma’a.

Namadi ya ce, “yayin da aka samu zanga-zangar lumana ta sauya zuwa tarzoma ta hanyar lalatawa da satar dukiyar al’umma da ta Ƙasa, ba za mu amince wa hakan ba don baya cikin al’adarmu, saboda haka ba za mu lamunta ba.”

Ya ƙara da cewa, za su cigaba da aiki da hukumomin tsaro don tabbatar da kiyaye dukiyoyi da rayukan al’umma daga sharrin ɓata-gari a faɗin jihar.

By Babaji