
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Sarkin Kano na 16, Alhaji Muhammadu Sanusi II ya yi kira ga al’umma da kar su bari a yi amfani da su wajen kawo hargitsi a Kano da Arewa da ma a Nijeriya baki ɗaya.
Sarki Sanusi ya yi jawabin ne bayan da aka sake dawo da gudanar da zanga-zangar duk da dokar hana fita da gwamnatin jihar ta sanya saboda tashin-tashina da aka samu a ranar Alhamis.
Ƴan zanga-zangar sun sake taruwa a Tudun-Wada da ke Ƙaramar Hukumar Nasarawa tare da cigaba da yin zanga-zangar duk da dokar kulle na sa’o’i 24 da gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf ya sanya.
A wani taron ƴan jarida da aka yi a Fadarsa na Gidan Rumfa, Sarkin ya nuna damuwarsa kan yadda aka salwantar da dukiyar al’umma da sace-sacen kayayyakinsu da sunan zanga-zangar lumana kan tsadar rayuwa.
