Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja
Mataimakin shugaban ƙasa, Sanata Kashim Shettima a yau ya buɗe taron tattaunawa na shekarar 2024 a tsakanin masu ruwa da tsaki kan Nahiyar Afrika dangane da tattalin arziƙi.
Taron wanda aka buɗe shi yau a Otel ɗin (Transcorp Hilton), Abuja, cikin jawabin da ya gabatar ya bayyana tsare-tsare da matakan da gwamnati take ɗauka wajen hana karyewar tattalin arziƙin ƙasar a duniya.
Ya kuma yi kira kan samar da haɗin kai a duniya a tsakanin ƙasashen Afrika domin magance dukkan wani ƙalubalen tattalin arziƙi da kowace ƙasa take fuskanta tare da ribatar damammaki na cigaba.
“Na sani cewa Afrika ta na fama da ƙalubale kala-kala a fannin tattalin arziƙi, agaji, da rayuwar al’umma, ya zama wajibi ƙasashen da ke Nahiyar su ɗauki dukkan matakan da suka dace wajen sarrafa damammakin kan albarkatun ƙasa da bunƙasa rayuwar al’umma da ƙirƙira cikin aiki tare”.
Taken taron na bana shi ne “gudanuwar kasuwanci a tsakanin ƙasashen Afrika: dama ce ta ɗorewar bunƙasar tattalin arziƙi a Nahiyar Afrika”. Ta yadda kowace ƙasa za ta himmatu wajen bunƙasa cigaban Nahiyar ta fuskar tattalin arziƙi.
