Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris, ya bayyana cewa, Gwamnatin Tarayya ta hana sanar da cibiyoyin sayar da shinkafar da za ta bayar domin gudun kada wasu masu hannu da shuni su kawo matsala a tsarin.
Idris ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidan rediyon Abuja a ranar Larabar da ta gabata, inda ya bayyana shirin sayar da buhunan shinkafa mai nauyin kilogiram 50 kan kuɗi Naira 40,000, wanda gwamnati ta keɓance da nufin rage wa ‘yan ƙasa matsalar tattalin arziki.
A ranar Litinin ɗin da ta gabata ne dai ministan ya bayyana cewa gwamnati ta kafa cibiyoyin rarraba shinkafar a faɗin aasar inda ‘yan Nijeriya za su iya sayen shinkafar.
Sai dai a yayin wani ƙarin bayani na baya-bayan nan, Idris ya bayyana cewa, duk da cewa shinkafar tana nan ana shirin rarrabawa, ba za a bayyana ainihin wuraren ajiyar ta ba a halin yanzu saboda dalilai na tsaro.
“Ana cikin shirin rarraba wa jihohi daban-daban,” inji Idris.
“Wani lokaci, yana da wahala a ambaci hanyoyin da kuma lokacin saboda dalilan tsaro. Amma shinkafar ta riga ta samu, kuma za a sayar da ita a kan Naira 40,000 a wurare daban-daban a faɗin ƙasar nan.”
Ya kuma jaddada taka tsan-tsan da gwamnati ke yi wajen ganin shinkafar da aka ba tallafin ta isa ga masu cin gajiyar shirin. Ana yin taka-tsantsan don kada masu kuɗi su yi wawushe ta.”
Baya ga shirin rabon shinkafar, Idris ya bayyana sauran ƙoƙarin da gwamnatin Tinubu ke yi na inganta rayuwa a Nijeriya.
Waɗannan sun haɗa da asusun lamuni na ilimi na ƙasa da aka rattaba hannu kwanan nan, da nufin tallafawa ɗalibai miliyan biyu, tare da aikace-aikacen 120,000 da aka riga aka karɓa.
Ya kuma ambato asusun zuba jari na matasan Nijeriya na Naira biliyan 110, wanda zai gudana a cikin shekaru biyu masu zuwa, a wani ɓangare na dabarun gwamnati na magance ƙalubalen tattalin arziki.
