Hukumar Tace Finafinai: Yadda Abba El-Mustapha ya kawar da saɓanin siyasa a cikin Kannywood

Spread the love

Daga MUKHTAR YAKUBU KANO

(Ci gaba daga makon jiya)

MANHAJA: To duk da waɗannan ayyuka da ka gudanar, wacce babbar nasara ka samu a tsawon shekara guda da ka yi?

ABBA EL-MUSTAPHA: Babbar nasara da na samu ita ce ɗauke siyasa da na yi daga zukatan masu gudanar da harkokin su a cikin masana’amtar Kannywood, wannan ya sa, yau ga shi a Jihar Kano baki suna shigowa su gudanar da harkar fim wanda a baya sai dai a fita a je wani garin a yi, saboda wani yana ganin idan ya zo ya yi za a kama shi saboda siyasa, wani yana ganin idan ya yi waƙa za a kama shi a ci masa mutunci saboda bambancin siyasa, to yau wannan abin duk ya zama tarihi a cikin masana’amtar Kannywood, za ka zo ka yi sana’ar ka, amma abin da ake so kawai ka bi doka, babu wani cin zali ko cin zarafin wai don ba ɗan jam’iyyarmu ba ne. In dai ɗan fim ne kai kana da dama ka zo ka yi sana’ar ka cikin kwanciyar hankali tun da ƙaddarar mu ce mu zo mu yi sana’ar fim, to mu zo mu inganta ta mana. Wannan abin da maigirma Gwamna Abba Kabir Yusif yake so a yi kenan. 

Mu inganta sanarmu, wannan rigimar da ake yi da faɗace-faɗace ko a kulle mutum a yi kaza a yi kaza. In dai ba mutum ne ya yi laifin da ya kai a kira shi a yi masa hukunci a matakin gida ko matakin ƙungiya kuma ya nuna ya fi ƙarfin su, ba a tafiya ga kotu. Kuma idan an je ga kotu nan ma bai nuna nadamar sa ba, dole hukunci ya yi aiki a kansa. 

Amma abin ana bin sa daki daki, Babu cin zarafi, don mu so muke mu zo mu yi gyara da inganta sanarmu, kamar ni yanzu da na shafe sama da shekaru 25 a cikin harkar fim idan ban inganta ta ba ai ban yi mata gata ba. To zan zo na karɓi wannan kujerar kuma na ci gaba da yin abubuwan da ake yi a baya na amfani da kujerar wajen musgunawa ‘ya’yan masana’antar. Ai abin da na guda kenan, shi ya sa na shiga Kwankwasiyya. Don haka Kannywood ta zama waje da kowa zai zo ya yi sana’arsa, amma a bisa bin doka da oda.

Duk da irin wannan ayyuka da ka gudanar, akwai baton sabunta rajistar ‘yan fim da ake ganin ya tayar da ƙura a wannan Hukumar.

To maganar sabunta rajista wani abu ne da ya kasance aikin wannan hukumar ta tabbatar da ta yi wa duk wani mai gudanar da aikin sa da yake da alaƙa da wannan hukumar, kuma hakan ne zai bayar da damar a samu ƙididdigar mutanen da ake yin hudda da su, don haka babban aikin wannan Hukumar ta tace fim da kuma tsaftace shi, don haka yin rajistar ‘yan fim ya shigo ciki.

Don haka lokacin da na zo ina son na san adadin mutanen da suke cikin harkar fim saboda a gane ‘yan fim ɗin, don an kai matakin da kowa ya je ya yi laifi sai a ce daga cikin ‘yan fim ya fito. Kuma ni da kai kowa ya san ba ‘yan fim ba ne, don da na zo wannan hukumar an sha kira na a wasu hukumomi a ce an kama ‘yan fim, ina zuwa a matsayina da na shafe sama da shekaru 20 sai na ga ban san shi ba. Ban taɓa ganin su ba. Amma sun ce sun mallaki katin shaida na cewa su ‘yan fim ne amma ba ‘yan fim ba ne ba su da kamfani babu wanda ya san su a cikin harkar. To wannan abin na guda shi ya sa na ce a zo a sabunta rajista. To sai -yan ƙungiyoyin da suke cikin harkar fim irin su MOPPAN da Arewa suka ce na ba su dama wadda ba a taɓa bayarwa ba mana saboda ƙungiyoyin su yi ƙarfi, su ma waɗanda suke ciki su san ƙungiyoyin suna da ƙarfi kowanne a ba shi damar da ake ganin zai iya yin hukunci ba tare da an zo hukumar tace finafinai ba. 

Sai na ga ai wannan rage aiki ne, kuma ka bai wa ƙungiyoyin dama ba cewa in wani abu ne daga cikin su ka fito don haka a zo a ƙara samun damar da za a inganta harkar, don haka na yarda, Wanda shi ne karon farko da ‘yan fim suka fara samun damar su je su yi rajistar kansu, saboda ɗansu ne yake kan kujerar, duk abin da ɗan fim yake so shi nake yi masa a wannan kujerar, kuma ban ware ba, babu siyasa a ciki kowa ɗaya yake a wajena, saboda shi wannan muƙamin Allah zai iya ɗauka ya bai wa kowa a cikinsu.

Kuma haka za mu bi shi mu ba shi haɗin kai, haka aka yi a baya, ba a taɓa ji na ina yin takun saƙa da wani da yake shugabancin hukumar tace finafinai ba. Haka muka rinƙa yin aiki cikin jin daɗi da biyayya , don haka na ba su wannan damar ta yin rajistar ‘yan fim, to amma abin dai bai yiwu ba, ta yadda su ‘yan fim ɗin suka ƙi zuwa su yi rajistar kuma abubuwan sai na ga babu daɗi, na ce a ba ni harkar rajistar ya dawo ga hukuma domin ita tana da hukunci, don muna son mu san adadin mutanen mu don mu san yadda za mu yi mu’amala da su yadda za mu habbaka harkar fim. 

A matsayin ka na shugaba a Hukumar tace finafinai da ɗab’i ta Jihar Kano duk da girma na kujerar ka, amma sai ake ganin ba ka ajiye harkar ka ta fitowa a fim a matsayin jarumi ba, ko ya ya ka ke iya haɗa ayyuka biyu a lokaci guda?

To Alhamdulillah. Maigirma Gwamna ya zaɓo ni daga cikin ‘yan fim ya ba ni shugabancin Hukumar tace finafinai da ɗab’i ta Jihar Kano, wadda nake ta alfahari da hakan. Yau ga dan yana da ilimin da zai iya riƙe manyan kujeru na gwamnati. A she idan muka jajirce muka tsaya za mu iya zuwa ko’ina a duniya. Allah zai iya kaimu duk inda muke tunanin ba za mu je ba. Yau ga dan fim Ali Nuhu yana M D a Hukumar fim ta ƙasa. Wannan ya nuna ɗan fim yana da daraja a duniya a cikin al’umma da har zai iya riƙe waɗannan muƙamai.

Don haka Allah ya zaɓe ni ya ba ni wannan muƙamin hanyar maigirma gwamna, kuma lokacin da aka kira ni ma aka sanar da ni ina aikin fim ma a Abuja aka sanar da ni ga muƙamin da gwamna ya ba ka. To ka ga idan na ce zan katse wannan sana’a saboda na samu wannan kujerar ban yi mata adalci ba. Kuma ni kaina ban yi wa kaina adalci ba, kuma sauran furodusa da suka saka ni a cikin finafinan wanda yake mafi yawa masu dogon zango ne, to ka ga don na samu muƙami na ce su canza wani, ai ban yi musu adalci ba. 

Kuma shi muƙami da aka ba ni ya ta’alaƙa ne ga ‘yan fim. To idan na yi baya da su, ba zan samu abin da nake so ba . Amma dai duk da haka ina da tsari na ba zan je maka aiki a ranakun aiki ba , don haka idan zan yi maka aiki sai na ce ka saka mini Asabar ko Lahadi, a ciki na zaɓi lokaci na zo wanda daman an shirya kawai wajen da na fito za a yi, ni ɗan fim ne duk na san yadda ake shirya fim, don haka idan aka shirya duk abin ba zai bada wahala ba, wannan ya sa har yau babu wanda na juya na ce ba zan ƙarasa masa fim ɗin sa ba, saboda na samu matsayi, a a , don haka mu haɗu da ni da kai mu ƙara inganta aikin yadda gwamnati za ta yarda da abin da muke yi ta zo ta tallafa mana, wannan shi ne. 

Ba ka ganin wasu za su rinƙa kallon za ka yi musu tsada wajen ɗaukar ka aiki?

A a ba wai tsada ba ne, ai harkar fim ta Kannywood ba ta da tsada. Fim ɗin na nawa muke yi? Kasafin mu a fim nawa ne? Ai ba magana ce ta tsada ba. Magana ce ta kishi da kuma son abin, ai duk wanda na je aikin sa ya san kishin abin ne, don haka idan ma na ga furodusa mai wasa ne ba na yi. Amma maganar wata tsada ai ba ta taso ba, saboda fim ɗin na nawa muke yi. Kuma ni Ina ganin idan Allah ya rufa maka asiri to ka yi dace don haka ka manta da maganar tsada a nan.

Ganin ka samu shekara guda a kan kujera an gudanar da ayyuka, ko a yanzu me aka shirya don gudanar da aiki na gaba?

To ni daman mataki na nasara nake neman a kodayaushe .Ta ya za a yi ita masana’amtar Kannywood ta fita daga cikin ƙangin da take ciki na tattalin arziki da kuma tarbiyya da mu’amala. Kuma a yanzu kamar yadda na faɗa a baya, ko mata da muke yawan samun matsala da su a baya suke so su samu dama su zo su yi ta yin abubuwan da ba su dace ba a doshiyal midiya yau abin ya fara zama tarihi, abin da muke nema ya ci gaba kenan na tsaftace harkar. Kuma ya za a yi a inganta harkar fim. To yau fim ɗin Hausa ya fara shiga Netfliɗ, kuma yau ta kai manyan gidajen talbijin ‘yan fim ne suke zuwa su kai fim su biya a haska musu su je su nemo talluka . Mu daman irin wannan muke nema yadda za a kawo ci gaba don harkar fim ta ɗaukaka a duniya.

Don haka nake kira ga duk wanda yake son ya shigo harkar fim, to ya shigo da kyakkyawar niyya domin ya zo ya rufa wa kansa asiri. Amma duk wanda ya shigo da mummunar manufa yake son ya kai ga samun kaza da kaza ,to ya sani a kansa za ta ƙare. Amma dai abu muhimmi a fita neman ilimi mu goge da ilimi don ina cikin harkar fim na tafi na je na yi figiri na yi masters. Kai ba za ka iya ba, ke ba za ki iya ba, don za ka zo ka yi mu’amala da manyan mutane a duniya wanda ilimin ka ne zai ƙwace ka. Shi ne abin da nake nema a harkar fim.

Sauran kuma mutanen da suke ƙarƙashin hukumar kamar Sha’irai masu gidajen kallo, marubuta kowa ya tsaya a matsayin sa kuma ya inganta sana’arsa. Sannan ya zo ya haɗu da gwamnati wajen ganin an tsaftace harkar zuwa matakin nasara, don haka mu haɗa kai domin cimma nasarar da za ta samar da ci gaba mai ɗorewa.

Ina godiya ga maigirma Gwamna Abba Kabir Yusif da Jagora Sanata Rabi’u Musa Keankwaso da shugaban jam’iyyar mu ta NNPP da ‘yan fim abokaina da iyaye ƙanne da ‘ya’ya da suke cikin harkar fim da ‘yan uwa da abokai na gari iyayena da malamai na adduni da na boko duk ina godiya da irin gudunmawa da shawarwari da ku ke ba ni don haka nake cewa, Sai godiya.

Madalla mun gode.

Ni ma ina ƙara godiya sosai.

By ukarofi