
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Hukumar kula da masu yi wa Ƙasa hidima, NYSC ta gargaɗi ɗaliban da su ka kammala karatu a makarantun ‘polytechnic’ da ‘minotechnics’ cewa wajibi ne su gabatar da takardar shaidar yin horon IT na shekara ɗaya kafin ta karɓe su.
Shugabar hukumar reshen jihar Legas, Misis Yetunde Baderinwa ta faɗi hakan a yayin wani hira da jaridar ‘News Agency Nigeria’ a ranar Asabar a Legas inda ta ce hukumar ta fitar da takardar umarnin ne ga dukkan ɗaliban da hukuncin ya shafa.
Ta ce “sanannen abu ne cewa a kwanakin nan wasu daga cikin ɗaliban makarantun ba sa yin IT kafin shiga zangon karatun HND.”
Misis Yetunde ta kuma ce, dole sai ɗaliban sun yi IT kafin a ba su damar shiga zangon HND, ta na mai kira ga makarantun da su ke tabbatar da haka kafin ɗaukar su.
Ta ƙara da cewa, dokar za ta fara aiki ne daga sahu na gaba na masu yi wa ƙasa hidima inda ta ce ba za a bai wa waɗanda ba su cike sharuɗa ba damar yin rijista.
Kazalika, ta ce hakan zai taimaka wa nagartar harkar ilimi a Nijeriya.
