Tsohon shugan hukumar ƙwallon kafa ta Afirka CAF Issa Hayatou ya rasu. Hayatou, wanda ɗan ƙasar Kamaru ne, ya rasu saura kwana ɗaya ya cika shekara 78 a duniya a birnin Paris.
Hayatou ya kasance Shugaban ƙungiyar da yafi kowa jimawa kan karagar mulki. Ya hau kujerar a shekarar 1988 har zuwa 2017.
A lokacin shi, ƙwallon ƙafa a Afirka ta samu cigaba sosai, ɗaya daga cikin abun jajircewar da yayi shine kawo gasar kofin duniya Afirka karo na farko.
Ya taka rawa wajen ganin Afirka ta samu ƙarin gurbi a gasar cin kofin duniya.
Hayatou ya taɓa riƙe shugabancin hukumar ƙungiyar ƙwallo ƙafa ta duniya na riƙon kwarya bayan dakatar da shugaban ta a lokacin Sepp Blatter.
