Daga ALIYU SAMBA
Al’ada ce ta kafafen sada zumunta a duk sanda mutane suka karkata ƙarfin su akan wani lamari, za a yi ta samun fitowar bayanai da ko dai su tunzura mutane, ko kuma su fahimtar da su, a wannan yanayin kuma akan samu labarai na gaskiya da kuma na jabu da ake yaɗawa, don cimma wani hadafi, mutane kuma su yi ta yaɗawa bisa sani da rashin sani.
Kamar haka ne yanzu yake faruwa a daidai lokacin da wasu suka fake da yanayin da ’yan ƙasa ke ciki na tsanani sakamakon riƙon sakainar kashi da gwamnatocin baya suka yi wa ƙasar, suke tunzura matasa, don su samu damar cimma nasu hadafin. Ganin babu nasara a wancan fagen ya sa suka sauya linzami zuwa sabon batun mallakar rijiyoyin mai ga Tinubu.
Tabbas kamar yadda masu yaɗa waccan farfagandar ke faɗa, an sanya hannu kan yarjejeniya tsakanin kamfanin Oando da Agip a ranar 4 ga Satumba, 2023. Sai dai yarjejeniyar ba ta kai bantenta ba sai a kwanan nan sakamakon buƙatar wasu matakai da tsare-tsare na wajibi da ba a kammala cikawa ba. Za a gudanar da bikin sanya hannu kan tabbatar yarjejeniyar nan ba da jimawa ba.
Wasu mutane na son amfani da wani bidiyo na ɗan Bello (wani matashi mai amfani da kafafen sadarwa na yanar gizo) da kuma rubuce-rubuce da ake yi, don tabbatar da cewa a yanzu dukkan ragamar hada-hadar ɗanyen mai da shigo da tataccen mai na hannun kamfanin Oando, sai dai kuma sun manta cewa, har yanzu ma ba ta inda kamfanin Oando ke da cikakken iko akan gudanarwar kamfanin na Agip da kuma abubuwan da ya samar a shekarar 2023.
Ya kamata mai karatu ya karanta wannan gaɓar da kyau, kamfanin Oando ya na samun ganga miliyan 11 na ɗanyen mai a shekara daga Najeriya. Ta yaya kenan zai zama kamfanin da ke tace dukkan man Najeriya da ke samar da ganga miliyan 552.84 a kowacce shekara?
A kowacce rana, Nijeriya na samar da ganga miliyan 1.51 na ɗanyen mai, idan aka ɗauki wancan lissafin na ganga miliyan 11 a shekara na Kamfanin Oando, zai zama ganga 30,000 kamfanin ke samu a kullum, ta yaya wanda ke samun ganga 30,000 cikin ganga miliyan 1.51 ke riƙe da ragamar hada-hadar man ƙasar nan?
Idan ana magana akan kamfanoni da ke hada-hadar ɗanyen mai a ƙasar nan, kamfanin Agip ba ya cikin manyan kamfanoni 10 na farko na ƙasar nan. Manya kamfanoni biyar na farko su ne kamfanin Mobil da ke samun ganga miliyan 58, NPDC wanda yanzu ake kira NNPCL E&P ke samun ganga miliyan 50.5, sai kamfanin SNEPCO da kuma SPDC da ke samun ganga miliyan 45, sai CHEɓRON da ke da ganga miliyan 38, sai na biyar kamfanin Total E&P mai ganga miliyan 38. Kamfanin Nigeria Agip, wanda ya samu ganga miliyan 5.7 ne a shekarar 2023, ta yaya kenan yarjejeniyarsu da kamfanin Oando za ta sa Oando riƙe ragamar haƙo mai a Najeriya?
Mu dawo maganar fitar da ɗanyen mai zuwa ƙasashen waje da ake son nuna wa ’yan Najeriya cewa garin da bai kai girman Legas ne ke tace man da ake kawo wa Najeriya, ƙasashen biyar da aka fi kai man Nijeriya a duniya bisa rahoton watanni huɗu na farkon wannan shekarar ta 2024 su ne; Faransa, Isfaniya, Netherland, Indiya da kuma Amurka, wanda mafi yawan abinda ake fitarwa shine ɗanyen mai da kuma iskar gas (Natural Gas). Malta ba ta cikin wurare 10 da aka fi fitar da ɗanyen man Najeriya.
Wannan na ƙaryata masu yaɗa cewa, Shugaba Tinubu na amfani da ikonsa wajen fitar da man Nijeriya zuwa Malta, don a tace shi ko kuma a ɓoye, kamar yadda ake ta yaɗawa, don shafa wa gwamnatin baƙin fenti.
Sa’annan ko da ma kamfanin Malta mallakin Tinubu ne, kamfanin na samar da kaso 11 cikin 100 ne na tataccen man da ake shigo da shi zuwa ƙasar nan, akwai kaso 89 da ke shigowa daga wasu wuraren. Ta yaya mai shigo da kaso 11 cikin 100 zai zama shine ke kwashe dukkan kuɗin da aka ware na tallafin mai na Nijeriya?
Ba na mamaki idan na ga ana amfani da irin wannan ”Cheap Propaganda”, don aibanta gwamnati, amma tun bayan lalacewar matatun mai mallakin Gwamnatin Najeriya ba a yi wata gwamnati da ke hoɓɓasa da ƙoƙarin farfaɗo da su ba kamar wannan gwamnati, kuma mu na da kyakkyawan fatan cewa, nan zuwa shekara mai zuwa matatun man mu za su fara aiki, wannan zai taimaka wajen rage fita da shi zuwa ƙasashen ƙetare, a tace mana mu siya, kuma sai rage farashin mai a faɗin ƙasar.
Aliyu Samba shine mai taimaka wa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa kan Harkokin Yaɗa Labarai
