
Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI
Rundunar ‘Yan sanda a jihohin arewacin Nijeriya ta fara gudanar da bincike kan masu zanga-zangar da aka kama a yayin kwanaki 10 na zanga-zangar tsadar rayuwa a faɗin ƙasar.
Yayin da aka gudanar da zanga-zangar cikin lumana a kudanci, an samu ɓarkewar rikici da sace-sacen ababe da dama a Arewa wanda hakan ya sa aka sanya dokar hana fita a wasu jihohin yankin.
Aƙalla mutane 17 ne aka samu rahoton cewa sun rasa rayukansu a jihohin Abuja, Kano, Neja, Borno, Jigawa da Kaduna yayin da aka samu da dama da suka samu raunuka wanda hakan ta kai ga ƙungiyar kare haƙƙin ɗan-Adam ta Amnesty International ta yi alla-wadai da yadda ake amfani da ƙarfin hukuma wajen hargitsa masu zanga-zangar inda ta ke zargin jami’an da kashe mutum 21 a ranar farko ta zanga-zangar.
Sai dai rundunar ƴan sandan, ta ce ta kama masu zanga-zangar ne saboda ɗaga tutar ƙasar Rasha a lokacin da suka sauya akalar gangaminsu a jihohin Kano, Gombe, Kaduna, Katsina, Yobe, Bauchi, Borno da Jigawa inda ta ce za ta yi bincike akan su.
A ranar Litinin ne za a fara gurfanar da waɗannan aka kama a gaban kotu domin su fuskanci hukunci.
