Babu hujjar Arewa ta riƙa fama da talauci – Kashim Shettima

Spread the love

Mataimakin shugaban ƙasa Shettima ya musanta zargin da a ke cewa Shugaban ƙasa ya na nuna halin ko in kula ga Arewacin Nijeriya ganin yadda yankin ya ke da albarkatu da yawa.

A wata tattaunawa da yayi da rediyo Faransa ranar Lahadi, ya bayyana cewa Arewacin Nijeriya ta na gaba wajen manufofin gwamnatin Tinubu.

Ya cigaba da cewa, gwamnati na dagewa domin ganin ta inganta yankin Arewacin Nijeriya, duba da gwamnatin tarayya ta fitar da biliyan 100 domin inganta aikin noma.

Ya cigaba da cewa gwamnatin ta ƙara mafi ƙarancin albashi daga dubu 30,000 zuwa 70,000. Kuma gwamnati ta ƙirƙiri hukumar kula da cigaba Arewa maso Yamma da buɗe ma’aikatar kiwon dabbobi.

Don haka ya ce bai kamata a rinƙa danganta Arewacin ƙasar da talauci ba, domin Allah ya albarkaci yankin.

By ukarofi