Kotu ta ƙara wa’adin keɓance zanga-zanga a filin MKO Abiola na Abuja

Spread the love

Daga BELLO ABUBAKAR BABAJI

Alƙali Sylvanus Oriji na babbar kotun tarayya da ke Abuja, ya ƙara wa’adin umarnin dakatar da taron masu zanga-zanga a filin wasa na MKO Abiola wanda aka fi sani da ‘National Stadium’.

Mai shari’ar ya bayar da umarnin ne sakamakon shigar ƙara da babban lauya, Dakta Ogwu Onoja (SAN) ya yi a madadin Ministan Abuja, Nyesom Wike.

A lokacin yin hukunci game da ƙarar, babu ɗaya daga cikin mutane 12 da aka shigar da sunayen su akan ƙarar da ya bayyana kuma babu halstaccen wakilci daga gare su.

Waɗanda aka zayyano su acikin takardar ƙarar sune; Omoyele Sowere, Damilare Adenola, Adama Ukpabi, Tosin Harsogba, Sufeto Janar na ƴan sanda, kwamishinan ƴan sanda, Darakta-Janar na SSS, Darakta-Janar na ‘Civil Defence’, shugabannin rundunonin sojin ƙasa da na sama da na ruwa da wanda ba a bayyana sunansa ba.

Ministan Abuja ta hannun lauyansa, ya nemi Alƙalin da ya duba kalaman Damilare Adenola na barazanar cewa akwai yiwuwar a ƙara kwanakin zanga-zangar kan kwanaki 10 da aka amince da farko.

Onoja ya kuma ce, tunda babu ɗayan su da ya hallarci zaman kotun, ba a san kuma wani mataki su ke shirin ɗauka ba a nan gaba, yana mai cewa sun nemi hakan ne saboda tabbatar da an samu wanzuwar zaman lafiya a Abuja.

Daga ƙarshe, Alƙalin ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 22 ga watan Agusta domin sake wani zama akan batun.

By Babaji